✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A Takaice… 8

Yau za a yi jadawalin Gasar Cin Kofin Duniya A yau Juma’a ne ake sa ran Hukumar shirya kwallo ta duniya FIFA za ta fitar…

Yau za a yi jadawalin Gasar Cin Kofin Duniya

A yau Juma’a ne ake sa ran Hukumar shirya kwallo ta duniya FIFA za ta fitar da Jadawalin Gasar Cin Kofin Duniya da zai gudana a shekara mai zuwa a kasar Brazil.
kasashe 32 ne za a kasu su shiyya-shiyya don kowacce ta san kasar da za ta kece-raini idan aka fara gasar.
Kocin Najeriya, Stephen Keshi ya yi fatar kada Allah Ya hada kungiyar kwallon kafa ta  Super Eagles da kasashen Brazil ko na Italiya a wannan mataki.
Haka shi ma kocin Ingila Roy Hodgson ya yi fatan kada Allah Ya sa ’yan kwallonsa su hadu da na Brazil ko Italiya a wannan mataki.
Tuni kasashen da suka haye gasar suka zuba ido don ganin yadda Jadawalin zai kaya.
Kamar yadda Hukumar ta sanar, ana sa ran manyan bakin da aka gayyato zuwa wurin bikin su kimanin dubu 1 da 300 ne za su halarci bikin yayin da ake sa ran ’yan jaridu su kimanin dubu 2 don halartar bikin.
Da misalin karfe 5 na yamma agogon Najeriya ne ake sa ran za a fara gudanar da bikin.

 

Kamfanin Audi ya raba wa ’yan kwallon Real Madrid motoci

A ranar Litinin da ta wuce ne kamfanin kera motoci na Audi ya rabawa daukacin ’yan kwallon kulob din Real Madrid da ke Sifen motocin garari a matsayin kyauta.
Shi dai kamfanin yana daya daga cikin kamfanonin da ke daukar nauyin kulob din Madrid a harkar kwallo.
Shahararren dan kwallon Madrid mai suna Cristiano Ronaldo ne ya karbi mota mafi tsada da kamfanin ya ba su.  An kiyasta motar kirar Audi RS6 Abant kudinta ya kai Yuro dubu 129 kwatankwacin Naira miliyan 29.
Sai dan kwallo dabi Alonso ya karbi motar da kudinta ya kai Naira miliyan 21 yayin da Sergio Ramos da Iker Casillas aka ba su motocin da kudinsu suka kai Naira miliyan 20 kowannensu.
Shi kuwa koci Carlos Ancelloti ya karbi tasa motar ce da aka kiyasta ta kai Naira miliyan 19.
Haka kuma Gareth Bale da Fabio Coentrao da Angel Di-Maria da Sami Khedira da Illarramedi da Isco da Jese da Marcelo da Modric da Nacho da Pepe da Benzea da Arbeloa da kuma Morata an kiyasta kudin motocin da aka ba su a kan Naira miliyan 13 yayin da aka ba berane motar da kudinta ya kai Naira miliyan 9.
Tuni daukacin ’yan kwallon suka karbi makullan motocinsu bayan nuna farin cikinsu ga kamfanin.