✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abdul-Rahman Bida: Makahon da ke dillancin motoci daga Turai da Amurka

Abdul-Rahman Awwal Bida yana daya daga cikin fitattun dillalan motoci inda ya kafa Kamfanin Mahashura a garin Minna kuma jama’a da dama na hulda da…

Abdul-Rahman Awwal Bida yana daya daga cikin fitattun dillalan motoci inda ya kafa Kamfanin Mahashura a garin Minna kuma jama’a da dama na hulda da shi don shigo musu da motoci daga Amurka da Turai, duk da cewa shi makaho ne. Mai kimanin shekara 30, bayan dillacin motoci Abdul-Rahman malami ne a Makarantar Koyar da Nakasassu ta Jihar Neja.
A tattaunawarsa da wakilinmu ya ce kimanin shekara hudu da suka gabata ya koyi yadda ake shigowa da motoci daga Turai da Amurka. Kuma ya ce shigarsa wannan harka ta sa ya bude wa matasa hanyar samun aikin yi, duk da ba ya dauke su ne don ya rika biyansu albashi ba. “Ka san harkar kasuwanci a wasu lokuta na da matukar wahala kuma ba a cika samun kasuwa yadda ya kamata ba. Idan ka dauki mutum aiki wata ya kare ka kasa biyansa, ka ga ka tauye masa hakkinsa. Wannan ya sa muka shiga yarjejeniyar biyansu bisa tsarin kaso kaza na abin da aka sayar daga kowace mota,” inji shi.
Ya ce hanyoyin da yake tuntubar kamfanonin motocin da yake hulda da su, sun hada da hanyar sadarwa ta intanet da kuma waya, inda suke magana da Turawa domin sanin irin motocin da suke da su a kasa. Muddin ya binciko wannan da zarar mai bukata ya zo da kansa ko kuma ya nemi bayani ta intanet ko waya, ya yi masa bayanai dalla-dalla ya gamsu kuma ya bukata, sai ya biya rabin kudin, ya biya saura da zarar an shigo da motar.
Abdul-Rahman Bida ya kara da cewa, bayan an shigo da motar, yakan sa ma’aikatansa wadanda sun dade a cikin harkar kuma sun san irin abubuwan da yake la’akari da su, sai su duba masa sosai. Bayan ya gamsu da bayanan da ya samu kuma an gwada motar, sai ya kira wanda ya nemi a shigo masa da ita ya kawo cikon kudi ya dauki motarsa.
Game da irin mutanen da suke bukatar motoci daga wurinsa, Abdul-Rahman ya ce, “Ka san ita kasuwa tana hada mutum da mutane daban-daban a kusa da nesa. Wasu da ke sa ina shigo musu da motoci, ba a nan Minna suke da zama ba. Lokuta da dama ina samun aiki a Abuja, kuma sau da yawa gwada ni suke yi su ga ko da gaske ne ina iya shigo da motocin da suke bukata, Allah cikin ikonSa ina cin gwajinsu.”
Ya ce yana iya shigo da motocin da yawansu suka kai 100 daga kasashen Turai muddin za a ba shi rabin kudin a hannu. Kuma bai taba shigo da motar da aka samu akasi ba, tun daga lokacin da ya fara wannan harka fiye da shekaru biyu da suka wuce, sai dai ya ce bai taba samun tayin shigo da motoci daga ma’aikatu ko hukumomin gwamnati ba.
Abdul-Rahman Bida ya ce babban abin da ke ci masa tuwo a kwarya shi ne, yadda mutane ke tsangwamar jama’ar da Allah Ya yi wa nakasar wani bangaren jikinsu kuma suka nuna suna sha’awar gudanar da harkokin rayuwa kamar kowa.Ya ce, “Wani mutum ya sa aka kira ni zuwa Abuja domin mu shigo masa da mota, ina zuwa na ce masa na iso, sai ya ce kai Abdul-Rahman nake so in gana da shi, ya kirgo Naira 10 sai na tambaye shi wannan na mene ne? Ya ce min sadaka ce na  ba ka, na ce masa ba abin da ya kawo ni ke nan ba, ni ma ina bayar da sadaka ga mabukata.”
Ya kuma nuna takaici kan yadda jama’a musamman Musulmin Arewa suka mayar da bara sana’a suna alfahari da ita. Ya ce, “A wannan zamanin abin bai tsaya ga nakasassu kadai ba, hatta marasa nakasa sun mayar da bara sana’a, wasu babu tsoron Allah suna hadawa da karyar rashin lafiya da rasuwar wasu daga cikin iyalansu, ko ka ji wata na cewa mijinta ne ya rasu, ko kuma yana kwance a asibiti duk don a samu abin duniya.”
Ya ce a ’yan kwanakin nan ya fara shiga harkar gine-gine baya ga sayar da motoci, inda yake aikin da ya shafi rufin gida da kawata shi ga kuma aikinsa na koyarwa.