✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abdulaziz Yari ya zama Sanata

  Hukumar zaben Najeriya reshen Zamfara ta ayyana gwamnan jihar Abdulaziz Yari Abubakar a matsayin mutmin da ya yi nasara a zaben kujerar dan majalisar…

 

Hukumar zaben Najeriya reshen Zamfara ta ayyana gwamnan jihar Abdulaziz Yari Abubakar a matsayin mutmin da ya yi nasara a zaben kujerar dan majalisar dattawa a mazabar Yammacin Zamfara. Baturen zaben yankin ya ce Gwamna Yari na jam’iyyar APC ya samu kuri’a 153,626 yayin da abokin hamayyarsa na jam’iyyar PDP, Lawan Hassan, ya samu kuri’a 69,293 kamar yadda BBC ta rawaito.