✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ke tsakanina da Rahama Sadau – Yaseen Auwal

Yaseen Auwal, Darakta ne kuma Shugaban Kamfanin Shirya Fina-Finai na UK Entertainment, a hirar da ya yi da Aminiya a makon jiya ya bayyana irin…

Yaseen Auwal, Darakta ne kuma Shugaban Kamfanin Shirya Fina-Finai na UK Entertainment, a hirar da ya yi da Aminiya a makon jiya ya bayyana irin alakar da ke tsakaninsa da Rahama Sadau da dalilin da ya sa mutane suke ganin yana da zafin rai. Daraktan ya kuma bayyana kudirinsa na shirya fim a kan Boko Haram. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Wane ne Yassen Auwal?

Sunana Yaseen Auwal, an haife ni a Unguwar Sarari a Karamar Hukumar Dala da ke Jihar Kano.  A nan Dala na yi makarantar firamare da sakandare, daga baya na yi kwas din aikin jarida (Mass Communication) a Jami’ar Bayero  (BUK) da ke Kano.

Me ya ja hankalinka ka shiga harkar fim?

A gaskiya na dade da fara fim, na fara da matsayin jarumi ne, wato tun lokacin da kamfanin shirya fim na Sarauniya Film Production suke daukar fim dinsu da su jarumi Gagare, idan ban manta ba wajejen 1994 zuwa 1995 ke nan. Ka ga shekaru ne masu yawa. Daga baya sai na fara shirya fim a shekarar 2000, inda kuma a 2001 na fara ba da umarni.

A baya a gaskiya fitowata a fim ta kuruciya ce, tunda ba wani shekaru ne da ni ba. A lokacin shekarar 2000 kuma mun kara yin wayo sai ni da wadansu abokaina muka hada kudi muka fara shirya fim, da za mu yi fim na biyu ne na ce zan fara ba da umarni, kuma tunda ina bibiyar yadda ake daraktin, ina bin darakta Sidi Ishak Sidi tunda shi ne ya yi mana daraktan fim dinmu na farko da muka yi. Bayan na nemi shawararsa a kan ina so in fara bayar da umarni sai ya fada mini abubuwan da ya kamata in yi, daga nan na fara daraktin a shekarar 2001.

Idan an ambaci Kannywood wane abu ne yake fara zuwa maka rai?

Idan aka ambaci Kannywood farin ciki ne yake zuwa zuciyata, babu abin da zan ce sai godiyar Allah. Sannan idan aka ambaci Kannywood a ko’ina ne hankalina zai koma kai, ko karatu nake yi a kafafen sada zumunta (social media) idan na shiga ina ganin an rubuta Kannywood ko mene ne sai na tsaya na duba in ga me aka ce a kanmu. Ina son masana’antata, a nan nake sana’a, ina son ci gabanta sosai.

Zuwa yanzu wadanne matsaloli kake fuskanta musamman ma ta bangaren ba da umarni?

A gaskiya babu wata babbar matsala da zan ce ina fuskanta, domin duk abin da na sa a gaba zan yi shi nake yi, kuma ina samun nasara a kai.

Me za ka ce game da jita-jitar da ake yadawa cewa akwai soyayya a tsakaninka da jaruma Rahama Sadau?

Soyayya tsakanina da Rahama Sadau babu ko kadan. Ni na kawo Rahama Sadau Kannywood, ni na fara sa ta a fim, tun daga lokacin da na fara sa ta a fim muke da kyakkyawar alaka, har kawo yanzu kuma babu wani abu zan ce ta yi mini na rashin kyautatawa. Tana mutunta ni, tana ba ni daraja, ina zama da ita sosai. Muna zama mu yi shawara, don yanzu kafin in fara waya da kai ma na dade ina magana da ita ta waya, duk da cewa tana Saudiyya. Alakar da ke tsakaninmu mutane suke gani kamar soyayya ce a tsakaninmu, amma ba haka ba ne.

A cikin fina-finan da ka yi wanne ka fi so, kuma me ya sa?

Duk fim din da na yi daraktin to ina sonsa, saboda ba na yin fim sai na ji ina so labarin, sai na karanta labarin fim din, na ji kuma ina sonsa sai in yi shi. Amma fim ya samu daukaka wannan kuma daga Allah ne. Haka ne ni ma a cikin fina-finan da na yi wani fim din ya fi wani samun daukaka ko fin kasuwa.

 Yaseen tare da Rahama da kuma Mawaqi Umar M. Shareef
Yaseen tare da Rahama da kuma Mawaqi Umar M. Shareef

Wane fim dinka ne ya fi ba ka wahala?

Idan har ka kalli fina-finan da nake ba da umarni, yawancinsu masu wahala ne, ba na daukar fim mai labari kawai wanda za a ce ‘Action and Cut’. Ina so in yi labarin da zan sha wahala, irin fim din da kafin a dauki fitowa daya ma sai an sha wahala. Misali fim dina mai suna ‘Mati A Zazzau’, a Bauchi muka dauki fim din, fim din ya hada jarumai masu yawa, ga labarin da wahala. Fim din ‘Wani Gari’ ma ya ba ni wahala. Wani lokaci mutane za su kalli fim ma su ga kamar bai bayar da wahala ba, amma a wurin daukarsa an sha wahala.

Wani abu ne na farin ciki ya faru da kai a Kannywood da ba za ka taba mantawa da shi ba?

A gaskiya ba zan ce ga shi ba. Saboda abubuwan da suka faru da ni na farin ciki a Kannywood sun fi na bacin rai yawa. Domin in samu nasara bayan na yi fim ma abin jin dadi ne a wurina, musamman ma idan na ji mutanen gari suna cewa fim ya yi kyau.

Mutanen da suke cikin Kannywood da wajenta suna ganin kamar kana da zafin rai, me za ka ce kan haka?

Duk wanda zai yi hira da ni sai ya ce mini ina da yawan fada, ba fada ba ne magana ce ta gaskiya. Mu al’adarmu ta Hausawa idan ka kasance kana tsaye a kan magana ta gaskiya, ko magana daya ko idan aka maka ba daidai ba, sai ka fito ka fada wa mutum cewa ka yi mini ba daidai ba, sai a ce mutum mafadaci ne. Amma lokacin da za a yi maka ya dame ka a zuciyarka ka kasa furta shi sai a rika cewa wane yana da hakuri, amma ka cutar da kanka. To a gaskiya ni ba haka nake ba, ba na cutar da kaina, idan ka yi mini abu zan fada maka.

Idan an zo lokeshin ba zancen na san ka ko ka san ni, ko wata alaka, aiki kawai muka zo yi, idan an kammala a yi wasa da dariya, amma lokacin aiki ba na wasa ko dariya. Tabbas ana yin raha, amma ba na yarda wani ya zo da abin da zai bata mini aiki.

A kwanakin baya ka yi wani fim mai suna ‘Nisan Kwana’ har kuka saki wasu hotunan da aka dauki jarumi Sadik Sani Sadik da Rahama Sadau a matsayin mata da miji, ko me ya saya kuka yi haka?

A gaskiya na yi haka ne don in tallata fim dina da na zauna da furodusan fim din, furodusa ne a kamfanina mai suna UK Entertainment, sai muka ga dacewar yin haka, domin ba wani abu ba ne duk lokacin da za ka yi fim, sai ka tsaya ka yi tunani ta yadda za ka tallata fim dinka.

Wannan tambayar da ka yi mini ma ita ta tuna mini cewa wayar da muka yi da Rahama Sadau ma mun yi ta ka yadda za mu tallata fim din ‘Mati A Zazzau’ da fim din ‘Nadiya’ ne, akwai wani fim ma da zan yi mai suna ‘Matar Mutum’, duk fim din da ka yi sai ka yi tunanin abin da za ka yi wanda zai janyo hankalin mutane gare shi, har su ce ga wani fim mai suna kaza har ma su so su kalla.

Dalilin hakan ne a fim din ‘Nisan Kwana’ muka ce bari mu yi hotunan, tunda fim din yana da alaka da biki, a nan muka yi hotunan kafin aure, muka sake su a gari, inda ya ja hankalin mutane, kuma sai mu saki sunan fim din.

A shekarun baya ka saki fostar wani fim mai suna ‘Aliko’, inda jarumi Sadik Sani Sadik ya yi shiga irin ta shugaban ’yan Boko Haram, Abubakar Shekau, a yanzu batun ya yi sanyi ko me ya jawo hakan?

Bayan fostar ta fita sai muka samu korafe-korafe daga wurin mutane musamman abokan sana’armu, domin hankalinsu ya tashi da suka ga fostar tana da alaka da Shekau, suka rikice suna tsoron kada mu yi irin wannan fim din, amma a yanzu haka ana sake fasalin labarin saboda ya dan kwana biyu. Sannan kullum abubuwa suna faruwa, zamani na kara sauyawa, za mu yi fim din babu gudu babu ja da baya.

Ko wani jigo fim din ya kunsa?

Fim ne da zai wayar da kan mutane a kan mutane su daina shiga kungiyar ta’addanci, ba wai gaba daya fim din na tafiya a kan Boko Haram ba ne, magana ne a kan aikata miyagun laifuffuka, ba wai kawai a sa mutane a gurbatattun kungiyoyi  da ake jingina su da addini ba.