✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa a yanzu Buhari yake rayuwar nadama — Solomon Dalung 

Buhari mutumin kirki ne wanda ya aminta da makusantansa amma suka bata masa suna.

Tsohon Ministan Wasanni da Ci gaban Matasa, Solomon Dalung, ya yi ikirarin cewa a halin yanzu tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yana rayuwar nadama kan yadda makusantansa suka bata masa suna a lokacin shugabancinsa.

Dalung wanda ya yi aiki a gwamnatin Buhari, ya ce gwamnatin ta gaza wajen cika alkawuran da ta daukarwa ‘yan Najeriya a lokacin yakin neman zabe na shekarar 2015.

A hirarsa da gidan Radio Trust, tsohon ministan ya ce a matsayinsa na wanda suka kafa jam’iyar APC ya zama wajibi ya fadi gaskiyar abin da ke faruwa.

“Babu wani lungu da sako na kasar nan ba mu shiga a lokacin yakin neman zabe ba musamman a Arewacin Najeriya, mun dauki alkawura amma babu alkawarin da muka iya cikawa.

“Idan aka waiwaya baya, za a lura cewa babu wani abu da muka tsinana a lokacin gwamnatinmu.”

Ya ce a lokacin yakin neman zabe, sun yi wa ‘yan Najeriya alkawarin samar da tsaro da farfado da tattalin arzikin kasar da kuma yakar cin hanci da rashawa, amma sai dai sun gaza cika duk alkawuran da suka dauka.

Dalung ya bayyana Buhari a matsayin mutum nagari kuma shugaba mai gaskiya, wanda kuma ta aminta da mutanen da ke tare da shi, duk da cewa su ne suka bata masa suna.

“Buhari mutumin kirki ne wanda ya aminta da duk makusantansa saboda tsammaninsa duk mutanen kirki ne, amma a yanzu a dalilinsu yana rayuwa cikin nadama.

“Saboda su ne suka kai shi suka baro suka bata masa suna, sannan suka hana gwamnatinsa rawar gaban hantsi,” in ji Dalung.

Tsohon ministan ya ce gwamnatin jam’iyar APC daga tsakanin shekarar 2015 zuwa 2019 ta samu nasarori, domin al’amuran tsaro a lokacin ba su tabarbare kamar yanzu ba.