Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Abin da ya sa ba zan miqa kai ga ’yan sanda ba – Dino Melaye

Sanata Dino Melaye, da ke wakiltar Kogi ta Yamma, ya yi magana daga inda yake boye, inda ya  ce idan ya kai kansa ga ’yan sanda, Babban Sufeto, Idris Ibrahim zai iya yi masa allurar kisa domin ya kashe shi.

Sanata Melaye ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter shekaranjiya Laraba, yana misalta abin da yake fuskanta da irin abin da ya ce Annabi Elijah ya fuskanta kamar yadda aka ba da labari a cikin Baibul.

ADVERTISEMENT

Fiye da mako guda ke nan ’yan sanda suna kewaye da gidan Dino, suna neman kama shi bisa zargin hannunsa a fashi da makami da kuma yunqurin kisa.

Wannan ne karo na huxu da ’yan sanda suka yi yunqurin kama shi a 2018. Melaye ya ba da labarin yadda Baibul ya ba da labarin Annabi Elijah, wanda ya gudu ya boye a kan Tsaunin Carmel, bayan da Sarki Ahab na zamaninsa ya nemi kashe shi, saboda tsage gaskiyar da ya riqa yi.

ADVERTISEMENT

“Ni ba tsoron fitowa nake yi ba. Kuma akwai bambanci tsakanin tsoro da yin taka-tsantsan ko kaffa-kaffa.” Kamar yadda ya ce a Twitter.

Melaye wanda ya sauya sheqa zuwa PDP, dama yana fuskantar tuhumomi na shari’a da ’yan sanda suka gabatar da shi a kotuna biyu da suka haxa da yunqurin kashe kansa da kansa da zargin bai wa ’yan daba miyagun makamai. Amma kuma duk an bayar da belinsa a shari’un biyu.