✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa har yanzu Buhari bai nada ministoci ba – Faruk Aliyu

Alhaji Faruk Adamu Aliyu na daya daga cikin makusantan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari. Ya ce babu wadansu masu hana ruwa-gudu a gwamnatin Buhari. Kuma ya…

Alhaji Faruk Adamu Aliyu na daya daga cikin makusantan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari. Ya ce babu wadansu masu hana ruwa-gudu a gwamnatin Buhari. Kuma ya tabo wasu korafe-korafe da jama’a ke yi kan gwamnati, inda ya yi albishir kan wasu ayyukan alheri da ya ce gwamnatin za ta yi:

Ka kasance daya daga cikin makunsantan Shugaba Buhari, me ke faruwa har yanzu ba a nada ministoci ba?

Assalamu alaikum, akwai abubuwa da dama. Na farko akwai korafi kan kura-kurai da aka yi kan yadda tafiyar ta kasance a baya. To sakamakon haka ake ta tuntubar juna a tsakanin bangarori mabanbanta da ake ganin sun taimaka wajen sake samun nasarar zaben. Ba ana cewa za a iya gamsar da kowa ba ne, amma ana ganin hakan zai rage korafin da ya faru a baya.

An yi tsammanin samun gagarumin sauyi musamman a bangaren wutar lantarki, inda wadansu ke kiran a soke sayarda  kamfanin, mai za ka ce?

Kasan yadda tsarin gwamnati yake, shi ne ci gaba da abubuwa. Ba yadda za a ce duk wani abu da aka samu a gwamnatin da ta gabace ka, a ce za a soke shi, domin yakan iya zama alfanu. Dole sai an yi bincike a kansu wadanda suka sayi kadarorin kamfanonin wutar lantarkin nan sun saye su ne kan wasu yarjejeniyoyi da dokoki. Ashe dole sai an bi a hankali tare da yin taka-tsantsan. Sai dai abu guda da ya kamata a yi la’akari da shi, shi ne gwamnatin nan ta yunkuro wajen inganta wannan bangare. Misali shi ne babban aikin masana’antar samar da wutar lantarki ta Mambila da aka fara aikin, sai na Kashambila da aka karasa.

Ga kuma dimbin sababbin tashoshin rarraba wutar nan da dama da aka kafa. Ka san dama babbar matsalar ba wai samar da wutar ba ce, yadda za a rarrabata ya fi zama kalubale. Saboda wayoyin da ake amfani da su wajen loda wutar don rarrabata wasu ba za su iya daukar nauyin karfin wutar da ake samawarwa ba a kasa a lokaci guda, saboda matsalar kankanta ko jimawa. To gwamnatin nan tana yin aiki a wannan bangare.

Wani abu da muka ankarar da Shugaban Kasa a kai kuma shi ne, hade Ma’aikatar Wutar Lantarki da na Ayyuka da Gidaje a waje guda, hakan ya yi yawa kasancewar kowannensu babban ne da gwamnati ke son ta kawo sauyi a kai. Kuma muna kyautata zaton zai raba su, akalla ta wutar lantarki a yi mata ma’akatarta daban. Ko ba komai idan aka inganta wannan bangare kadai tamkar an sama wa mutane ayyukan yi ne. Saboda a dalilin haka masu masana’antu manya da kananan da sauran masu sana’o’i a cikin al’umma, za su tafi da sana’o’insu cikin sauki da samun riba. Shugaba Buhari ba ya da wani buri da ya wuce yadda zai inganta yanayin kasar nan da l’ummarta, kuma alhamdulillahi jama’ar kasa sun fahimci hakan kasancewar sun sake zabarsa, kuma insaha Allahu ba zai ba su kunya ba.

Akwai korafin cewa gwamatinsa ta fi maida hankali a kan manyan ayyuka kadai a maimakon surkawa da kanana da suka fi taba tattalin arzikin talaka saboda irin ministoci da ya dauko yaya wannan batu?

Wannan ba gaskiya ba ne saboda gwamnati na ayyukan gina gidaje a dukkan jihohin kasar nan. A wasu wuraren tana yin su ne ita kadai wasu kuma na hadin gwiwa ne da kamfanoni. Sannan shi kansa manyan ayyukan irin su titi wanda tun kafuwar kasar nan ba a taba ganin irinsa ba a lokaci guda, tare da biyan tarin basussukan da gwamnatocin baya suka ci a wajen kamfanonin.

Aiki ne da ke tafiya da injiniyoyi da supabaizan hanyoyi da leburori, baya ga masu kananan sana’o’i da ke samu kudin shiga ta dalilinsu irin masu abinci. Ga layin dogo da aka karasa na Abuja zuwa Kaduna da na Itakpe zuwa Warri da na Legas zuwa Ibadan wanda nan da wata daya za a fara hawansa. Sannan kafin karshen bana za a sauya akalan aikin layin dogon ya koma shiyyar Kano ya taho Kaduna don hade shi da wanda ya nufo Abuja. Gwamnati za ta yi haka ne don ganin aiki ya ratsa kowanne sashin kasa. Aikin titin mota da na layin dogo da aka yi daga Legas zuwa Ibadan yana matsayin tamkar zuciyar kasar ce saboda muhimmancinsa, kasancewar ta can ne ake dauko mafiya yawan abubuwa da ake shigowa da su zuwa sassan Kudu maso Yamma ko Kudu maso Gabas da nan Arewa. Kuma ta can din ne dai ake fitar da kaya zuwa waje. To gwamnatin Buhari ce ta sake yin aikin hanyar da kuma layin dogon. Sannan a bangaren Arewa, titin mota da ya taso daga Kano zuwa Kaduna har Abuja, na matsayin titi mafi muhimmanci da ya sada Arewa da Kudu da wasu sassan Arewa da Birnin Tarayya, yanzu haka ana aikin titin tare da fadada shi a bangarori daban-daban. Sannan na layin dogo za a jingine aikinsa a Ibadan a dawo da aikin bangaren Kano kamar yadda na yi bayani mutane da yawa sun samu ayyukan yi. Hakan zai sama wa wannan shiyya ta Arewa aikin yi, baya ga dimbin jama’a da za su amfana da shi. Gwamnati na yin wadannan ayyukan ne daki-daki saboda ba ta da isassun kudin da za ta hada ayyukan gaba daya a lokaci guda. Idan ta yi haka dole sai ta yi watsi da bangaren lafiya da ilimi da aikin gona da sauransu, wanda ka san hakan ba abu ne mai yiwuwa ba. Kuma maganar da ake cewa an dauko ministoci wadanda ba su san matsalar al’umma ba, ba gaskiya ba ce. A duk minstocin da Shugaba Buhari ya dauka a wannan bangare na Arewa da ake cewa da yawansu ba su san matsalar al’umma ba, daga wadanda suka tsaya takarar Gwamna tun muna CPC ne sai wadanda suka rike mana shugabancin jam’iyya.

Wadansu na zargin cewa Gwamnatin Buhari ba ta sauraron koke-koken jama’a, misali shi ne bukatar a sauya hafsoshin tsaro da kawar da ’yan hana ruwa gudu a fadarsa, me za ka ce?

To ni ma a ra’ayin kashin kaina ni Faruk Adamu Aliyu, na gamsu da a sallami shugabannin tsaron nan gaba dayansu, a sauyasu da wadansu. Ba don komai ba sai don a magance matsalar tauye hakkin na bayansu, wadanda a  yanzu duk sun yi ritaya sun bar su. To irin haka na jawo korafi musamman a gidan soja, sannan duk wata basira da ta kamata su nuna ta kare. Sai dai hakika an samu ci gaba a kan yadda suka samu lamarin tsaron, amma ai bin ka’idar aikin zai iya kawo karin nasarar. Kuma ina tabbatar maka cewa ni a kashin kaina na yi magana da Shugaban Kasa a kan wannan lamari, kuma daya daga cikin bayanin da ya yi mini wanda ni da kai da ba ma bangaren tsaro, ba lallai ne mu fahimci hakan ba. Daga cikin abubuwan da ya yi bayani a kai shi ne, a duk lokacin da ake cikin halin ta-baci, to ba a sauya kwamandan yaki farat daya, saboda kawai wadansu sun bukaci a yi hakan. Haka nan shi Shugaban Kasa yakan samu wasu rahotannin tsaro da sauran jama’a ba za su ji ba. Sai dai ina tabbatar da cewa kamar yadda nake kyautata zato, shi kansa Shugaban Kasa a wannan karo zai sake duba lamarin, saboda  wa’adinsu ya jima da kaiwa, ya sauya wadannan hafsoshi. Sannan akwai maganar da ake yi ta wai wadansu “cabal” ko ’yan hana-ruwa-gudu. A gaskiya akwai rainin wayo a lamarin a ce wai akwai wadansu masu fada- a-ji a fada, sai abin da suke so za a yi, wannan ba gaskiya ba ce. Shugaban Kasa da ka gani kamar inji yake a kullum ana tsara masa wadanda zai gani da abin da zai yi kuma a karfe kaza. Haka nan ba gaskiya ba ce a ce ministocinsa da suke aiki a karkashinsa ba sa iya ganinsa sai dai wadannan mutane. Mu ma da ba aikin muke yi ba, muna ganinsa. Illa dai kowace gwamnati akwai wadanda take tafiya da su kamar yadda aka gani a baya. Ya kamata jama’a su san cewa akwai zumunci akwai aminai kuma akwai mutanen da kake tare da su, ba yadda don ka samu gwamnati shi ke nan sai ka ce ba ruwanka da su. Sai dai fa ina tabbatar maka idan ma har akwai wasu “cabal” a wannan gwamnati, to Buhari shi ne cabal din kansa. Domin babu wani mutumin da ya isa ya sauya masa ra’ayi a kan abin da ba ya so. Kuma bari mu yi abin baro-baro, a cikin cabal din nan ana kawo maganar Malam Mamman Daura, to, ni ina ganin ana zaluntarsa kuma watakila ana dauke masa alhaki ne. idan gaskiya ne abin da ake fada a kan Mamman Daura cewa shi ne mai sawa, shi ne mai hanawa. To ai ga Sambo Dasuki wanda matsayin uwa daya uba daya yake ga matar Mamman Daura kasancewar, su ’ya’yane ga marigayi Sarkin Musulmi Ibrahim Dasuki, kumar ’yar uwar Sambo Dasukin nan ita ce kadai mata ga Mamman Daura. Ashe idan zai iya sa Shugaba Buhari ya yi wani abu, da sai ya sa ya saki Sambo Dasuki. Illai dai ya kamata mutane su san cewa dan uwansa ne kuma suna tare tun kafin a kafa gwamnati. Mu din nan wadansu  na cewa mun kanainaye shi. Gaskiyar magana ita ce duk wanda ya san shi, ya san tare muke. Tun lokacin da idan mun fito sai mutane suke yi mana dariya. To yanzu idan an ganmu tare sai a ce mun zama cabal, wannan maganar mutane ce kawai, kuma ba za ka hana su fadin albarkacin bakinsu ba.

Jam’iyyarku ta samu nasarar rike shugabancin a majalisun dokokin tarayya, yaya za ka bayyana yadda za ku ribaci haka?

Ko ba komai, ba ma jin za a sake samu jinkiri wajen amincewa da kasafin kudi har ya kai wata 6. Sannan su kansu ’yan majalisar ba ma jin za su yi cushe irin yadda na baya suke yi, ko su zuba kudi ga kawunansu da sunan ayyukan mazabu sannan a ki yin aikin, don sun san za a yi bincike a kai. Ko a sa ayyuka marasa kan gado a tsakuri kudin kasafi a sayi babura don raba su ga jama’a maimakon su bar gwamnati ta yi aiki da kudin yadda ta tsara. Kuma Shugaban Kasa ba yi da wani zabi dole sai dai ya sa wa dokar kasafin kudin hannu, in kuma ya ki a yi ta zama haka nan. Wadannan shugabannin majalisar da ma tun baya, su ne jam’iyya ta zaba amma aka butulce mata, su kuma suka yi hakuri suka ci gaba da yi mata halacci, to ga shi su ma a yau ta yi musu halaccin.

A karshe masu nazari kan al’amuran siyasa na ganin cewa yadda jam’iyyarku ke zabubbukan fitar da gwani wajen dauki-dora na iya kai ta ga wargajewa da zarar wa’adin mulkin Buhari ya kare?

A gaskiya ban yarda da wannan hasashe ba. Na farko dai shi kansa Shugaba Buhari ba zai yarda ya bari jam’iyyar da ya yi amfani da ita ba, ya samun mulki  wa’adi biyu ba ya bar ta ta wargaje ba bayan wa’adin mulkinsa ya kare. Ko ba komai zai so a ce wani daga cikin aminansa ne ya ci gaba da mulkin don dorewar manufofin jam’iyyar da gwamnatinsa ta fara aiwatarwa. Sai dai na yarda an samu wasu matsaloli a wasu wuraren inda shugabanni suka yi abin da suka ga dama. Sai dai kada ka manta saboda shi dinne a kan mulki ya karfafa wa kotu ta yi abin da ya dace kuma ga shi kana ganin ana ta warware zabubbukan. Misali shi ne abin da ya faru a Zamfara, idan kamar gwamnatocin da suka gabata ne hakan ba zai faru ba. Kuma ga yadda ya faru a Adamawa da Bauchi da sauransu, kuma hakan shi ne daidai, shi ne dimokuradiyya.

Sai dai duk da wannan adalcin da kuke cewa kun yi jama’a, sai ga shi kun gaza yi wa naku kamar yadda ya faru a zaben majalisun dokoki na Bauchi da Edo?

Abin da ya faru a wadannan jihohi ba zai dore ba. Ba yadda za a yi wanda ke da ’yan majalisa 8 ya yi nasara a kan mai 20 kamar yadda ya faru a Bauchi. Sai dai da yake gwamnati ce mai bin ka’ida ba za a je da jami’an tsaro a warware wannan lamari ba, dole a bi abin kan tsari kamar yadda shari’a ta tsara. Kuma na tabbatar kotu za ta warware.