✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa harshen Hausa ke kara bunkasa a duniya –Farfesa Powlak

Farfesa Nina Powlak malama ce da ta shafe sama da shekara 40 tana koyar da Harshen Hausa a Jami’ar Warsaw da ke kasar Poland. A…

Farfesa Nina Powlak malama ce da ta shafe sama da shekara 40 tana koyar da Harshen Hausa a Jami’ar Warsaw da ke kasar Poland. A kwanakin baya Jami’ar Bayero da ke Kano ta karrama ta kan gudunmawar da ta bayar wajen koyar da Harshen Hausa a Nahiyar Turai, Aminiya ta tattauna da ita, inda ta bayyana dalilin da Harshen Hausa ke bunkasa a duniya:

 

Aminiya: Mene ne takaitaccen tarihinki?

Farfesa Nina: Kamar yadda kika ji sunana Farfesa Nina Pawlak kuma an haihe ni a ranar 10 ga Satumban 1950 a garin Ostrowak da ke tsakiyar Gabashin kasar Poland. Na yi karatun firamare da sakandare a garinmu. Bayan na kammala sai na tafi jami’a na karanta fannin Nazarin Afirka a matakin digiri na farko. Haka digirina na biyu na yi ne a wannan fanni inda na kammala a 1974. A 1980 na koma na yi digiri na uku a Ilimin Kimiyyar Harshe kan Harsunan Afirka inda na samu kwarewa a ilimin Harshen Hausa. Bisa tsarin ilimi na kasar Poland muna yin digiri na hudu. A wannan lokaci ma Harshen Hausa na zaba na ci gaba da yin nazari a kansa wannan ya faru a shekarar 2007.

Aminiya: Yaya aka yi kika koyi yin magana da Harshen Hausa?

Farfesa Nina: A lokacin da nake koyar da Harshen Hausa a Jami’ar Warsaw sai aka ba ni dama don in zo Najeriya in koyi harshen kamar yadda Hausawa ke magana da shi. Na zauna a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya tsawon wata shida, ina koyon yadda ake magana da Harshen Hausa. A wancan lokaci na kai ziyara wasu garuruwan Hausawa, musamman nan Jihar Kano. Kuma bayan na koma Poland na ci gaba da kawo ziyara Najeriya. Zan iya cewa na zo Kano sau shida.

Aminiya: Tsawon wane lokaci kika dauka kina koyar da Harshen Hausa?

Farfesa Nina: Na fara koyar da harshen Hausa tun bayan da na samu digirin farko, kuma har zuwa yanzu abin da nake yi ke nan. Na yaye dalibai masu dimbin yawa a can kasarmu da kuma kasashen ketare, Ko a nan Jami’ar Bayero na yaye dalibai da suka je neman digiri na uku da suka hada da Farfesa Hafizu Miko Yakasai da Dokta Isa Yusuf Chamo. Ban da wannan ina zuwa jami’o’in Afirka don duba ayyukan wadansu dalibai musamman masu yin digiri na uku.  Jami’ar Bayero ma ta gayyato ni na zo don daidaituwar wasu ayyuka. Akwai malamai da dama da za su duba wadannan ayyuka, a lokacin ne na duba aikin kundin digiri na uku na Farfesa Yakubu Magaji Azare. Har ila yau akwai wadansu dalibaina daga malaman Jami’ar Bayero da suka kammala digiri na uku a can wajenmu da suka hada da Dokta Jibrin Shu’aibu Adamu da Dokta Ahmad Shehu.

Aminiya: Me ya sa kika zabi yin nazari a Harshen Hausa a kan sauran harsunan Afirka?

Farfesa Nina: Lokacin da nake karatu na fara bincike a kan Harshen Hausa, sai na fuskanci cewa harshe ne mai ban sha’awa musamman ta fuskar nahawunsa. Hakan ya sa na mayar da hankali sosai a kan koyonsa.

Aminiya: Kin taba yin wallafe-wallafe cikin Harshen Hausa?

Farfesa Nina: Kwarai kuwa a yanzu haka na rubuta makaloli sama da 117. Daga cikin wadannan makaloli sama da 50 ko 80 da Hausa suke da ilimin kimiyyar harshen. Na yi littafi kamar 18. Cikinsu akwai wadannda aka rubuta da harshen Hausa da wadanda aka rubuta da Ingilishi saboda masu jin harshen da wadannda aka rubuta da harshenmu na Poland.

Aminiya: Yaya kike ganin matsayin Harshen Hausa a duniya?

Farfesa Nina: Babu shakka Harshen Hausa kullum ci gaba yake yana kara bunkasa. Kuma mutane suna sha’awar koyon harshen sosai musamman a can wurinmu, saboda yadda harshen yake da nahawunsa da duk wani abu da ya kunshi kimiyyar harshe.