Daily Trust Aminiya - Abin da ya sa mu tara Naira dubu goma-goma ga masu garkuwa –
Subscribe

Abin da ya sa mu tara Naira dubu goma-goma ga masu garkuwa – Mutanen Doka

Mazauna kauyan Kamfanin Doka da ke Karamar Hukumar Birnin Gwari sun bayyana cewa sun dora wa kowane gida a kauyen harajin Naira dubu goma don su  karo-karo su biya kudin fansar ’yan uwansu da ke hannun masu garkuwa da mutane da suke zaune a yankinsu.

A cewar mazauna yankin, masu garkuwar suna tsare da ’yan uwansu kusan mutum ashirin kuma sun bukaci a biya su Naira miliyan biyar domin su sako mutanen nasu.

Aminiya ta gano cewa al’ummar kauyen, wadanda akasarinsu manoma ne ba su da kudi kuma sun tara Naira miliyan uku da dubu 300, saura Naira miliyan daya da dubu 700 kudin su cika.

Wata majiya da ke yankin, da ba ta son a ambaci sunanta saboda dalilin tsaro ta shaida wa wakilinmu cewa yanzu ana bi gida-gida, kowa ya taimaka da abin da yake da shi domin a cika kudin fansar, a karbo mutanen.

Majiyar ta ce yawancin mutanen da aka kama manoma ne da suke zuwa zagayen gonarsu, sai kurum a yi garkuwa da su. “Abin da ke faruwa shi ne, akwai mutanenmu sama da ashirin da ake garkuwa da su. Su kuma masu garkuwa da mutanen sun bukaci a biya su Naira miliyan biyar amma mutanen kauyen Naira miliyan uku da dubu 300 suka iya tarawa, saura Naira miliyan daya da dubu  700, saboda ainihin dangin wadanda ake tsare da su ba su da kudi,” inji majiyar.

Game da ko masu garkuwar ne suka tilasta wa mutanen kauyan cewa tara masu kudi ko su kai musu hari sai majiyar ta ce “A’a, ba haka abin yake ba. Gaskiyar lamarin shi ne, gida-gida muke bi ana tara wadannan kudI da suka bukata a matsayin kudin fansar mutanen da suke hannunsu.

“Ai su wadannan mutanen yanzu ba ta hari suke ba, illa kurum su kama mutum su bukaci fansa. Yanzu haka wannan kudi da ake tarawa da nufin kai musu a matsayin kudin fansa, taimako ne kurum wadansu ke bayarwa a garin ba kuma tilasta musu aka yi ba.”

Wani mazaunin yankin wanda bai son a ambaci sunansa ya ce “Duk da kokarin da karamar hukumarsu ke yi domin inganta tsaro a yankin, har yanzu akan dan fuskanci rashin tsaro a wasu kauyukan. Amma maganar gaskiya ita ce, a yankin Doka mutane ne suka yanke shawarar bi gida-gida ko in ce suke yin karo-karo domin tara kudi su cikata saboda karbo mutanensu da ke hannu,” inji shi.

Ya ce hanyar Birnin Gwari zuwa Funtuwa, wadda ta ba ta biyuwa a watannin baya, an samu sauki a yanzu inda masu ababen hawa ke bi ba tare da an samu matsala ba.

“Yanzu an dan samu sauki a kan hanyar Birnin Gwari zuwa Funtuwa, domin mutane na wucewa ba tare da wata matsala ba sai dai kurum tsautsayi in ya rutsa da mutum, Allah Ya kyauta,” inji shi.

A kan ko an samar da jami’an tsaro a hanyar sai ya ce “Su masu garkuwa ne da kansu suka rage tare hanyar saboda su ma su dan samu saukin rayuwa,” inji shi.

texem
More Stories