✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa muka kai karar ’yan Majalisar Bauchi 18 kotu

Barista Mukhtar Abubakar Usman tsohon Kwamishinan Shari’a ne a Jihar Bauchi kuma shi ne lauyan ’yan majalisa 13 daga cikin ’yan Majalisar Dokokin Jihar Bauchi…

Barista Mukhtar Abubakar Usman tsohon Kwamishinan Shari’a ne a Jihar Bauchi kuma shi ne lauyan ’yan majalisa 13 daga cikin ’yan Majalisar Dokokin Jihar Bauchi da suke kalubalanci ikirarin da ’yan majalisar 18 na Jamiyyar APC  suka yi na bayyana Alhaji Kawuwa Shehu Damina a matsayin Shugaban Jihar. Wakilinmu ya tautauna da shi inda ya fayyace dalilinsu na zuwa kotu da halin da ake ciki:

Gashi kun shigar da kara a kotu har ta dakatar da bangaren abokan shari’arku da suke ikirarin su ne suke da shugaban majalisa, mene ne dalilin da ya sa kuka kai karar?

’Yan majalisa 13 da suka hada da ’ya’yan Jam’iyyar PDP da APC ne suka ba mu wannan aiki mu je kotu mu nema musu fassarar dokokin kundin tsarin mulkin kasa da kundin yadda ake tafiyar da majalisa a Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, suna so  bayan kotu ta yi fassara kuma ta dakatar da Alhaji Kawuwa Shehu Damina da Tukur Ibrahim daga bayyana kansu  a matsayin shugaban majalisa da mataimakinsa. Saboda yadda suka yi abin bai tafi da tsarin mulki ba, na farko tsarin mulki a sashi na 96 zuwa sashi na 106 sun gwada yadda ake zaman farko a majalisa da yadda ake zabe. Ya gwada cewa Akawun Majalisa  shi zai shugabanci zaman ya tsara gudanar da zabe a tsakanin mambobin majalisa, kuma sashin ya gwada cewa duk wani mataki da za a dauka na majalisar dokoki daya bisa uku na yawan ’yan majalisa ya isar. A Jihar Bauchi ana da ’yan majalisa 31 kuma an samu 13 ka ga an samu fiye da abin da ake bukata, saboda haka an saka rana Gwamna ya rubuta takardar bude majalisa an gaya wa kowa ranar 20 ga Yuni da karfe 10 na safe, ba su zo ba sai da lokaci ya kure kuma aka nada Shugaban Majalisa Abubakar Y. Sulaiman da Danlami Ahmad Kawule Mataimakinsa, saboda haka muke neman fassara a kan wannan abu da suka yi, ya yi daidai kuma mun gwada wa kotu ya yi daidai kuma abin da su kawowa na  sandar majalisa ba tare da ainihin sandan majalisar ba, a tsakar rana ba tare da shiga cikin zauren majalisa ba, kamar yadda doka ta tsara shin wannan zaben da suka yi ya yi daidai bayan an yi zabe, shi ne muke so kotu ta fassara kuma muna kokarin nuna wa kotu ta gane abin da suka yi ya saba wa tsarin mulki da tsarin tafiyar da majalisar dokokin. Amma kafin a ji kararmu saboda akwai abu na gaggawa wannan yana cewa shi ne shugaba wancan yana cewa shi ma shi ne shugaba sai muka nemi kotu ta dakatar da Alhaji Kawuwa Shehu Damina da Alhaji Ibrahim Tukur daga bayyana kansu a matsayin su ne shugabannin majalisar har sai an gama shari’a. Yanzu abin da aka sani shi ne bisa odar da kotu ta bayar bisa dokar kasa Alhaji Abubakar Y. Sulaiman shi ne Shugaban Majalisar Jihar Bauchi, Ahmad Kawule  Mataimakinsa.

An ce a zo karfe 10 amma su ’yan majalisar da kake karewa an ce sun yi zaben ne tun karfe shida na safe mece ce gaskiyar lamarin?

Wato abin da muka gabatar a gaban kotu shi ne karfe 10 na safe idan wani yana da wata takarda sai ya kawo ya ce ba karfe 10 ba ne. Ba ma son doguwar magana a kan abin da yake gaban kotu.

A siyasance wannan jinkiri ba ku ganin zai iya hana ruwa-gudu wajen gudanar da ayyukan gwamnati?

A’a ba zai hana ba saboda akwai odar kotu,  ya kamata a ce sun kawo sauran jama’arsu, su 18  su bi doka da odar kotu su rika zuwa majalisa ana aikin majalisa na kafa dokoki har sai abin da kotu ta ce. Ai ba fada ba ne,  ba yaki ba ne. Wadancan sun ce su ne suka yi nadin gaskiya, ku kun ce ku ne yanzu ana gaban kotu shi ke nan sai a dakatar da yin dokoki?

Amma Abubakar Sulaiman ya dage zaman majalisar sai abin da hali ya yi, kana zaton wannan ba zai kawo nakasu ga yi wa al’ummar Jihar Bauchi ayyukan da suka kamata ba? 

Ana yin haka wannan koda kotu ko babu kotu, wannan na fi zaton an yi haka ne saboda wasu dalilai da ba su shafi kotu ba. Akan yi haka kuma ba zai ajiye majalisar dokoki ta Jihar Bauchi har illa masha Allahu ba, akan fadi illa masha Allahu ne amma akan dawo mako daya ko kwana uku ko wata daya, ba za a yi ta wucewa har ya wuce hankali ya cutar da jiha ba, haka ba zai yiwu ba. Abin da ya kamata ’yan majalisa dukka suyi shi ne su zo su ba da goyon baya ko mutum yana kin zaben da aka yi waAbubakar  Sulaiman yana da kyau ya mai da wukarsa ya dubi Jihar Bauchi ya yi mata aikin da mutane suka zabe shi, har an gama shari’a. Kotu ba ta cikin siyasa ballantana ya yi tunanin za a yi masa manakisa. Kotu za ta bi gaskiya, idan mu ne masu gaskiya za a ba mu idan su ne masu gaskiya za a ba su gaskiya.

Ko akwai wani yunkuri na sasantawa a tsakani?

Yanzu dai ba mu ji ba amma sasantawa kullum yakan faru ko ana gobe za a yanke hukunci, amma yanzu ba mu ji ba kuma komai yana iya faruwa a siyasa.

A matsayin kuna lauyoyinsu ba za ku ba da shawarar a sasanta ba?

Aikinmu kullum idan mutum ya zo kafin mu shigar da kara sai mun duba idan akwai yadda za a sasanta ba tare da an yi ta zuwa kotu ba,sai mu yi.  ’Yan majalisar da muka kai kara abu na hannunsu idan maganar sasantawa ce ba mu za mu yi kara mu ce muna neman sasantawa ba, su da muka yi kararsu su ya kamata su dubi Jihar Bauchi su ce suna neman sasantawa.

Ku ’yan siyasa ana ganin rashin hadin kanku na daga cikin abin da ke kawo koma baya. Ana ganin cwannan matsala ta zama kamar karan-tsaye ga shirye shiryen gwamnati  a siyasance yaya kake ganin lamarin?

Ni dai a bangaren PDP akwai hadin kai, ka yarda da shugaban majalisa ka ba shi goyon baya daga wata jam’iyya ba adawa ya zamo shugaban majalisa akwai hadin kai da ya fi wannan? Haka akwai  wadansu daga APC su ma sun ba da goyon baya ga wannan tafiya sun hada kai da ’yan PDP an fitar da shugaban majalisa. Wadansu tsiraru ne da suka nace sai sun  hana Jihar Bauchi ci gaba sai sun yi yadda suke so a jihar su ne suke kulle-kulle a Abuja kuma siyasar Abuja ba za ta kai su ba.