✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa Najeriya za ta iya lashe Kofin Afirka na bana – Pascal

Mista Patrick Pascal (MON),  tsohon dan kwallon Super Eagles ne kuma yanzu haka mamba ne a Kwamitin Kula da Tsare-Tsaren Kungiyar a Hukumar Kwallon Kafa…

Mista Patrick Pascal (MON),  tsohon dan kwallon Super Eagles ne kuma yanzu haka mamba ne a Kwamitin Kula da Tsare-Tsaren Kungiyar a Hukumar Kwallon Kafa ta Kasa (NFF).  A zantawarsa da wakilinmu ya bayyana irin shirin da kungiyar ta yi game da fuskantar gasar cin Kofin Afirka da za a fara yau a kasar Masar da kuma irin ’yan kwallon da Super Eagles ta gayyato don kare mata muradi:

Wane irin shiri kuka yi don tunkarar gasar cin Kofin Afirka?

Yanzu abubuwa sun canja.   A baya masu ruwa-da-tsaki da su kansu ’yan wasan suna yin gaggawar a kira su don su yi wa Super Eagles kwallo don a lokacin ba maganar me za a samu ake yi ba, ana maganar kishin kasa ne.  Amma yanzu abin ba haka yake ba. Mafi yawan ’yan kwallon suna kallon me za su samu? Me za a biya su, don haka ba sa maganar kishin kasa. Sannan da yawa daga cikin ’yan kwallon da ake gayyatowa suna wasa ne a kasashe daban-daban na duniya. Sun riga sun yi kudi, don haka dan abin da Najeriya za ta ba su a ganinsu bai taka kara ya karya ba, don haka tilas sai an hada musu da lallashi don su ana biyansu ne a kowane mako, kuma makudan kudi suke karba, idan suka kwatanta da abin da suke samu a Najeriya ai bai taka kara ya karya ba. Wadansu ma suna ganin idan aka gayyato su su yi wa kasar nan wasa idan suka ji ciwo to zai iya shafar sana’arsu a inda suke buga kwallo, don haka wadansu ma ko an  gayyace su, ba sa son zuwa. Amma dai a halin yanzu Hukumar NFF ta kammala shiri tsaf kuma ta gayyato zaratan ’yan kwallon da za su kare mata muradi a gasar cin Kofin Afirka da za a fara yau Juma’a amma sai gobe Asabar Najeriya za ta fara wasanta na farko da Burundi.

To za a iya cewa kun shirya tsaf don tunkarar wannan gasa?

A gaskiya idan aka yi la’akari da irin shirin da Hukumar NFF ta yi zan iya cewa an shirya tunkarar wannan gasa. A da, ana gayyatar ’yan kwallo ne ana saura ’yan kwanaki kafin a fara gasa. Don haka da an tattara ’yan kwallon ba sa samun wani horo na musamman sai ka ga an fara gasa da hakan yake shafar kwazon ’yan kwallon. Hakan ke sa tun ba a je ko’ina ba ka ga an fitar da su daga gasar, don ba su ma fahimci junansu ba. Amma ganin yadda a wannan lokaci akan gayyaci ’yan kwallo ne a kan lokaci, su samu horo tare, a shirya musu wasannin sada zumunta daban-daban, hakan na sa su goge, su fahimci junansu kafin su tunkari kowace irin gasa.  Kuma a gaskiya na yaba da irin shirye-shiryen da kungiyar Super Eagles ta yi, kuma ina da tabbacin za ta iya lashe Kofin Afirka a wannan karo.

Me za ka ce game da fargabar da wadansu ke yi cewa da wuya kungiyar Super Eagles ta iya lashe kofi ganin mafi yawan ’yan kwallon suna yin wasa ne a kananan kulob a sassan duniya?

Abin dubawa a nan shi ne, ba dan kwallo ya yi kwallo a manyan kulob shi ne kadai ya cancanci ya buga wa kasarsa kwallo ba. Ana bukatar dan kwallon da zai sanya zuciya da kuma kishin kasa sai ka ga Allah Ya taimake shi. Kuma kasashe nawa ne suke takama da manyan ’yan kwallon da ke yin wasa a manyan kulob a sassan duniya amma sai ka ga wadanda suke amfani da ’yan wasan gida sun fi su kokari?  Misali fiye da rabin ’yan kwallon Afirka ta Kudu a gida suke yin wasa, haka abin yake a wasu kasashen da ke Afirka. Amma mu a Najeriya muna da ’yan kwallo a sassan duniya. Kokarin da kowanensu yake yi a kulob dinsa ne abin dubawa, ba wai girman kulob ba. Wilfred Ndidi, dan kwallon Najeriya ne da ke wasa a kulob din Leicester City na Ingila kuma yana daga cikin wadanda suka samu lambar yabo a gasar Firimiya ta Ingila a bana. Kulob din da yake yi wa wasa ai ba wani babba ba ne, amma idan ka dubi irin kwazon da ya nuna a kakar wasa ta bana, dole a gayyace shi saboda irin kwazonsa.

Don haka abu  muhimmi a nan shi ne kokarin da ’yan kwallon za su yi ne abin dubawa ba kulob din da suke yi wa kwallo ba.  Wasu kasashen ma daukacin ’yan kwallonsu a gida suke yin wasa, to su kuma sai su ce ba za su halarci kowace gasa ba saboda ba su da ’yan kwallo a manyan kulob na duniya?

Wane kwarin gwiwa kake da shi a kan Najeriya ce za ta dauki wannan kofi a bana?

Gaskiya ina da kwarin gwiwar kungiyar Super Eagles ce za ta zama zakara a bana ganin yadda muke takama da zarata kuma matasan ’yan kwallo.  Mafi yawa daga cikin ’yan kwallon Super Eagles a halin yanzu matasa ne, masu jini a jika. Alal misali dubi matashin dan kwallo Samuel Chukwueze da ke kwallo a kulob din Billareal na Sifen, duk da irin kwazon da yake da shi, ba ya cikin ’yan kwallo 11 da ake fara wasa da su (Starting 11) a Super Eagles. Ire-irensa suna da yawa a kungiyar. Kuma a halin yanzu harkar kwallo tana yi ne da matasa a ko’ina a duniya. Sannan babu kungiyar da take shiga wata gasa da niyyar idan ta je za a doke ta, za ta shiga ne da niyyar ta samu nasara, to haka ake so, idan kuma ta samu akasin haka, to sai ta rungumi kaddara ta koma gida ta ci gaba da shiri.

Cin hanci da rashawa na daya daga cikin abubuwan da ke kawo koma baya a harkar kwallon kafa, me za ka ce?

Wannan abu ne da ke faruwa a fadin duniya wanda ka ga ni da wanda aka kama shi ne barawo amma yau a duniya ina ne mutum zai je a ce ba a yin cin hanci da rashawa?

Ita Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) da zarar ta kama wani jami’i ko dan kwallo da laifin karbar cin hanci da rashawa za ta kafa kwamiti kuma ta ba mutum damar ya kare kansa. Idan bai kare kansa ba to a nan ne za ta dauki mataki a kansa. A halin yanzu akwai wadanda suke fuskantar hukuncin hukumar daban-daban.  Wadansu an dage su na tsawon lokaci, wadansu kuma an dage su daga shiga harkar kwallo har abada. Amma dai abin akwai takaici a ce matsalar karbar cin hanci da rashawa ta shiga harkar kwallon kafa.

Wace shawara za ka ba gwamnati game da harkar wasanni?

Shawarar da zan ba gwamnati ita ce ta yi kokarin cire hannunta daga harkar wasanni ba kwallon kafa kawai ba. Kasashen da suka ci gaba irin Ingila, gwamnati ba ruwanta da harkokin wasanni, tana dai sanya ido ne ta ga yadda ake gudanar da harkar.  Kamfanoni masu zaman kansu da masu hannu da shuni ne suka mallakar kungiyoyin wasanni, inda suke samar da kudin shiga masu yawa ga gwamnati. A kasashen Sudan da Nijar akwai kungiyoyin kwallon kafa da dama da masu hannu da shuni da kamfanoni masu zaman kansu ne suka mallaka. Kuma ga kungiyoyin suna yin kwazo a fagen kwallon kafa a Nahiyar Afirka.

To me zai hana a samu irin haka a Najeriya mu da ake ganin mun fi kowace kasa yin fice a Nahiyar Afirka a bangaren wasanni musamman a bangaren kwallon kafa?

Sai dai wadansu ba sa son a ce gwamnati ta tsame hannunta daga harkar wasanni ne saboda abin da suke samu. Tuni aka tura bukatar yin haka ga Majalisar Dokoki ta Kasa, an yi karatu na farko da na biyu amma har yanzu an kasa yin karatu na uku don ta zama doka.  Ka ga akwai lauje cikin nadi. Amma muddin ana so harkar wasanni ta bunkasa a kasar nan, to sai gwamnati ta tsame hannunta, ta bar abin a wajen ’yan kasuwa, inda za su rika samun riba, yayin da gwamnati kuma za ta rika samu kudin shiga.