✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abokan ango su 7 sun rasu a hadarin mota jim kadan da shafa Fatiha

Wadansu abokan ango su bakwai sun rasu jim kadan da kama hanyar komawa gida bayan sun halarci daurin aurensa. Abokan angon wadanda suka fito daga…

Wadansu abokan ango su bakwai sun rasu jim kadan da kama hanyar komawa gida bayan sun halarci daurin aurensa.

Abokan angon wadanda suka fito daga garin Bokkos a Jihar Filato sun yi hadarin ne a kusa da garin Toro da ke Jihar Bauchi bayan sun baro garin Magama Gumau da ke Karamar Hukumar Toro da ke Jihar Bauchi inda aka daura auren a ranar Asabar da ta gabata. Wannan hadari ya jefa al’ummar garin Bokkos cikin tashin hankali da dimaucewa lokacin da suka samu labarin aukuwarsa.

Abokan angon da suka rasu wadanda matasa ne sun hada da Amadu Haruna da Sham’unu Ibrahim da Bashir da Hassan Tahir da Haruna Musa da Idris Rabi’u da kuma Abubakar Adam.

Sun gamu da hadari ne a kusa da garin Toro, lokacin da suka dawo daga daurin auren abokinsu, mai suna Aminu Garba da amaryarsa Zainab Abdullahi wadanda aka daura musu a garin Magama Gumau a ranar Asabar din.

Da yake yi wa wakilinmu bayani kan yadda lamarin ya faru, wani dan uwan matasan da ya halarci daurin auren mai suna Alhaji Adamu Muhammad (Chabori) ya ce sun taso daga garin Bokkos da ke jihar Filato ne suka je daurin aure a garin Magama Gumau da ke Karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi a ranar Asabar.

Ya ce bayan an daura auren, sun zauna sun ci abinci, sai suka ce wa abokan angon, su yi gaba suna zuwa domin su za su taho da amaryar.

Alhaji Adamu Chabori, ya ce da misalin karfe daya na rana, sai aka kira su a waya, aka ce musu ’yan uwansu sun yi hadari a hanya. “Nan take muka taso domin mu zo mu ga abin da ya faru. Kuma muna zuwa kusa da asibitin Toro a wata gangara, sai muka samu motar angwayen kirar Sharon ta fada a cikin wani rami,” inji shi.

Ya ce ana zargin motar ta kauce daga hanya ce saboda mugun gudun da direbanta yake yi.

Chabori ya ce mutum 8 ne a cikin motar, kuma mutum 7 sun rasu, direban ne kawai ya tsira inda yake kwance a asibiti.

“Da muka zo aka fito da su, sai aka kawo wata babbar mota aka debe su, a lokacin da aka fito da su mutum 3 sun riga sun rasu. A asibitin Toro ne sauran mutum 3 suka rasu, mutum daya kuma ya rasu a asibitin Plateau Hospital da ke garin Jos. Daga nan muka kwashi gawarwakinsu muka tafi da su garin Bokkos muka yi musu jana’iza a yammacin ranar,” inji shi.

Ya ce dukan matasan ’yan kasa da shekara 30 ne, kuma mutum 2 ne kawai suka yi aure daga cikinsu.

“A gaskiya abin da ya faru ya sanya mun dimauce a garin, maza da mata da iyaye baki daya, Musulmi da Kirista, saboda rasuwar matasan. Kuma da Kiristocin garin ’yan kasa da Yarbawa da Ibo aka je aka yi jana’izar matasan,” inji shi.

Da yake zantawa da wakilinmu kan lamarin angon, Aminu Garba ya ce ya yi matukar kaduwa da faruwar hadarin. Ya ce duk da yana wajen daurin auren, amma bai iya zuwa wajen da hadari ya faru ba.  “Wadannan matasa da hadarin ya rutsa da su, abokaina ne kuma muna tare a kowane lokaci,” inji shi.

Sakataren Kungiyar Matasan Karamar Hukumar Bokkos Kwamared Mabur Tokshik ya bayyana cewa hadarin da ya faru, wani babban abin bakin ciki ne ga al’ummar yankin baki daya.

Ya ce matasan da hadarin ya rutsa da su, matasa ne da ake tunanin nan gaba za su iya ba da gudunmawa wajen ci gaban yankin da kasa baki daya.

“Don haka a matsayinmu na shugabannin matasan yankin, muka fito baki dayanmu muka nuna juyayi kan wannan rashi da muka yi. Kuma muka tsaya wajen ganin an yi jana’izar matasan ba tare da nuna bambancin addini ko kabila ba, domin muna zaune lafiya da junanmu,” inji shi.