Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Abubakar Jinjir ya rasu a Yola

Mataimakin Sufeto janar na ’yan sandan Najeriya (AIG) na reshen “zone 3’’ a Jihar Adamawa ya rasu. Marigayi Jinjir ya rasa ransa ne a sakamakon hawan jini da ya buge shi a daren Asabar din da ta gabata.
Rahotanni sun nuna marigayin ya sanar da masu yi masa gadi ne halin da yake ciki inda aka garzaya da shi Babban asibitin kwararru na Yola FMC daga bisani Likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.
Kakakin ’yan sandan Jihar Adamawa, DSP Othman Abubakar ya tabbatar da mutuwar Jinjir. Koda muka tuntube kakakin yan sandan na jahar  “lallai an kai marigayin asibitin FMC na Yola a inda aka tabbatar da rasuwarsa a daren Asabar din da ta gabata sakamakon hawan jini”, inji shi.
Othman ya kwatanta marigayin a matsayin mutum mai kwazo da hazaka a wajen tafiyar da aikinsa.  Ya ce tuni aka kai gawar marigayin karamar Hukumar Rano da ke Jihar Kano kamar yadda iyalansa suka bukata.

ADVERTISEMENT