✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abubuwan da suka faru a ranar zabe a Jihar Oyo

Duk da yake Jam’iyar PDP ce ta lashe zaben Shugaban Kasa a zaben ranar Asabar a Jihar Oyo, sai dai Jam’iyyar APC da ke mulki…

Duk da yake Jam’iyar PDP ce ta lashe zaben Shugaban Kasa a zaben ranar Asabar a Jihar Oyo, sai dai Jam’iyyar APC da ke mulki a jihar ita ce ta yi nasarar lashe zaben kujera 2 daga cikin 3 na Majalisar Dattijai da 9 daga cikin kujeru 14 na Majalisar Wakilai a jihar.

Sakamakon zaben Shugaban Kasa daga kananan hukumomi 33 da Hukumar INEC ta bayyana a Ibadan ya nuna cewa PDP ta samu kuri’u dubu 366 da 690,  yayin da APC ta samu kuri’a dubu 365 da 229.

Gwamna Abiola Ajimobi wanda a ranar 29 ga watan Mayu mai zuwa zai cika wa’adin shekara 8 yana mulki a jihar, Jam’iyyar APC ta tsayar da shi dan takarar Majalisar Dattijai a mazabar Oyo ta Kudu, inda ya sha kaye a hannun Mista Kola Balogun na Jam’iyyarPDP. Sakamakon da Hukumar Zabe ta bayar ya nuna cewa Kola Balogun na PDP ya samu kuri’a dubu 105 da 720, yayin da Gwamnan ya samu kuri’a dubu 92 da 218.

Jim kadan da bayyana sakamakon zaben Gwamna Ajimobi ya  amincew da kayen da ya sha.

Bayanin amincewar Gwamnan ya fito ne a cikin wata takardar sanarwa a ranar Litinin da ta gabata. “Na amince da sakamakon da Hukumar INEC ta bayar kuma ina taya Kola Balogun na Jam’iyyar PDP murnar lashe zaben,” inji shi.

Sanarwar dauke da sanya hannun Mai ba Gwamna Shawara na Musamman a kan Harkokin Sadarwa, Mista Bolaji Tunji ta yi bayanin cewa Gwamnan ya nuna matukar farin ciki da jin dadi a kan yadda aka gudanar da zaben na ranar Asabar lami lafiya a Jihar Oyo da yadda al’ummar jihar suka fito kwai da kwarkwata suka nuna soyayya ga APC da kaunarsu ga Shugaba Muhammadu Buhari da suka kada masa kuri’a tare da sauran ’yan takarar Majalisar Dokoki ta Kasa da APC ta tsayar a jihar.

Ya yi kira ga al’ummar jihar su rubanya abin da suka yi a ranar 9 ga watan Maris mai zuwa wajen zaben Gwamna da wakilan Majalisar Dokokin Jihar.

Aminiya ta lura da wani muhimmin abu da ya auku a ranar Juma’a da ta gabata, jajibirin ranar zaben, inda wadansu ’yan takarar Gwamna; suka yi taro a Ibadan, suka tattauna yiwuwar taron dangi domin hana Jam’iyyar APC katabus a zaben na ranar Asabar, 9 ga watan Maris mai zuwa.

Tsohon Gwamnan Jihar, Adebayo Alao Akala kuma dan takarar Gwamna na Jam’iyyar ADP da dan takarar Gwamna na ADC Sanata Olufemi Lanlehin da dan takarar Gwamna na PDP Mista Seyi Makinde da dan takarar Gwamna na ZLP, Cif Sharafadeen Alli ne suka yi wannan zama don taron dangi ga APC, kuma masu sharhin siyasa sun ce  akwai alamar nasara a taron, idan aka lura da sakamakon zaben ranar Asabar.

Duk da yake sakamakon taron ya yi nasara a waje daya ta fannin hana Gwamna Abiola Ajimobi cin zaben kujerar Majalisar Dattijai, sai dai a waje daya kuma sun kasa cimma burin ganin ’yan takarar da jam’iyyunsu suka tsayar ne suka yi nasarar lashe kujerun sanatoci 2 daga jihar.

Wani abin sha’awa da ya auku bayan bayyana sakamakon zaben na ranar Asabar shi ne, irin yadda dukan shugabanni da kusoshin jam’iyyun siyasa suka rika tofa albarkar bakinsu a kan yadda aka gudanar da zaben lami lafiya a Jihar Oyo, ba kamar yadda aka zata ba.