Subscribe
 • facebook
 • twitter
 • whatsapp
 • linkedin
Abubuwan da ya kamata a sani kafin a je filin jirgin sama

Filin jirgin saman Legas

Abubuwan da ya kamata a sani kafin a je filin jirgin sama

Sanin kowa ne cewa ranar 8 ga watan Yuli za a dawo da zirga-zirgar jiragen fasinja a cikin gida a wasu daga cikin filayen jiragen saman Najeriya bayan kusan wata uku da dakatar da su.

Wata sanarwa da Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama ta fitar ta nuna cewa jirage za su fara zirga-zirga a wannan rana a filayen jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, da na Murtala Mohammed da ke Legas, da na Mallam Aminu Kano da ke Kano.

Su kuma filayen jiragen sama na Fatakwal, da Owerri, da Maiduguri za su bi sahu ne ranar 11 ga watan Yuli, yayin da sauran filayen jiragen saman za su ci gaba da hadahada ranar 15 ga wata.

Sai dai akwai wasu matakai masu muhimmanci da fasinjoji za su dauka kafin ko bayan sun shiga jirgi.

Duk wanda ya kasa daukar wadannan matakai to ba zai hau jirgi ba, don kuwa hukumomi za su sa ido sosai don tabbatar da bin matakan da nufin hana yaduwar COVID-19 a filayen jiragen sama.

Wadannan matakai su ne:

 1. Da farkon fari, a yi dukkan mai yiwuwa a guji tattaba abubuwa. Sannan a yi iyakar iyawa a kauce wa rabar ma’aikatan filayen jiragen sama.
 2. A isa filin jirgi sa’o’i uku kafin lokacin tashin jirgi, domin matakan da za a bi suna da yawa.
 3. A saka kyallen ko gilashin rufe fuska ko duka biyun a ko da yaushe – a filin jirgi da ma a cikin jirgi.
 4. A tsaya a kan alamun da aka yi na tsayawa a kowane lokaci. Tazarar da ke tsakanin alamun mita 1.5 ce.
 5. A je a yi wa kaya feshin maganin kwayoyin cuta a wuraren da aka tanada kusa da inda aka tanadi wuraren wanke hannu. An rage yawan mutanen da za su iya zama a wuraren da aka tanada don masu jiran jirgi daga 500 zuwa 250.
 6. A wanke hannu ko a yi amfani da man sanitizer don tsaftace hannu.
 7. Da an isa kofar shiga a ba da kai don gwajin zafin jiki.
 8. A cikin filayen jiragen a ba da tazara a ko da yaushe yayin da ake bin matakan bincike kafin hawa jirgi.
 9. Akwai kujerun da aka lika wa wasu alamu na Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Najeriya (FAAN). Yayin da ake jiran jirgin da za a hau, a guji zama a kan wadannan kujerun.
 10. A cikin jirgi ma akwai kujerun da ba a so a zauna a kansu. A kaurace wa zama a kansu a kowane lokaci.
 11.  Ba za a ba da abinci a jirgi ba don kada a cire kyallen rufe fuska. Amma za a ajiye wa fasinjoji ruwa saboda jin dadinsu.
 12. Idan mutum ya yi ta tari ko atishawa a filin jirgi ko a cikin jirgi za a killace shi, a kuma mika shi ga hukumomin lafiya na filin jirgi. Su kuma za su mika shi ga Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) don a yi masa gwajin COVID-19 idan akwai bukatar hakan. Idan ya zama dole mutum ya yi tafiya da wadannan larurori masu kama da alamun COVID-19, to ya rike sakamakon gwajin da aka yi masa mai nuna cewa ba ya dauke da cutar.

Ba su ke nan ba, amma idan aka kula da wadannan to za a wuce lafiya.

Matafiya, a dawo lafiya.