Da Dumi Dumi

Adamawa za ta gudanar da zaben kananan hukumomi a watan Nuwamba

Hukumar Zabe ta Jihar Adamawa ta ce za ta gudanar da zaben kananan hukumomin jihar a watan Nuwamba mai zuwa.

Shugaban Hukumar, Isa Shetima ne ya bayyana haka, sai dai bai bayyana ranar da za a gudanar da zaben ba. Shetima  ya ce za a bayyana ranar a nan gaba kadan, don haka ya bukaci jam’iyyun siyasa da suke da niyyar shiga zaben su fara yakin neman zaben tun daga shekaranjiya Laraba.

Hakazalika ya ce za a gudanar da zaben fidda ’yan takara daga ranar 31 ga Agusta zuwa ranar 7 ga Satumba, kuma a tabbatar duk jam’iyyun siyasa sun mika sunayen ’yan takararsu ga hukumar zuwa ranar 10 ga Oktoba.

Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya aike wa Majalisar Dokokin  Jahar kudiri a kan nada kantomomin riko a jihar wanda kuma majalisar ta amince da hakan, kuma aka           kaddamar da kantomomin kananan hukumomin a ranar 4 ga Yulin nan.

ADVERTISEMENT
Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya