✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

AFCON 2019: ’Yan Ghana sun ci mutuncin Alkalin da ya hura wasansu da Tunisiya

Jim kadan bayan Tunisiya ta doke Ghana a bugun fanareti a gasar cin Kofin Afirka a ranar Litinin da ta wuce ne magoya bayan kungiyar…

Jim kadan bayan Tunisiya ta doke Ghana a bugun fanareti a gasar cin Kofin Afirka a ranar Litinin da ta wuce ne magoya bayan kungiyar Black Stars ta Ghana suka shiga shafin sada zumuntar Bictor Gomes alkalin da ya hura wasan suka ci masa mutunci.

An tashi wasan ne da ci 1-1 da hakan ya sa aka yi bugun fanareti kuma Tunisiya ta samu nasara da ci 5-4.

Dalilin da ya sa magoya bayan Ghana suka ci zarafin alkalin wasan shi ne yadda a yayin wasan Kyaftin din Ghana Dede Ayew ya zura wata kwallo a ragar Tunisiya amma alkalin ya soke kuma ya ce ta taba hannun dan kwallon kafin ya zurata a raga.  Sai dai a wani nazari da aka yi bayan an kammala wasan, an nuna kwallon ba ta taba hannun Kyaftin din ba hasali ma bakinsa kawai ta goga.

Wannan dalili ya sa magoya bayan Ghana suka rika antaya wa alkalin wasan zagi da bakaken maganganu a shafin sadarwarsa na Instagram.

Rahotanni sun ce alkali Bictor Gomes ya yi matukar kaduwa lokacin da ya bude shafin sadarwarsa na Instagram ya ga yadda fiye da mutum 2000 a kankanen lokaci suka aika masa sakonnin zagi da na bakaken maganganu har sai da ya dakatar da shafin daga yin mu’amala da kowa sai wanda ya zaba.

Sai dai alkalin, dan asalin Afirka ta Kudu akwai yiwuwar ya kai Ghana kara a gaban Hukumar CAF don a bisa masa kadi game da wannan cin fuska.

Sau hudu Ghana ke lashe Kofin Afirka amma rabon da dauki kofin kofin tun a 1982 kimanin shekara 37 da suka gabata.