Da Dumi Dumi

AFCON 2019:  Yau za a yi wasan karshe a tsakanin Senegal da Aljeriya

A yau Juma’a da misalin karfe takwas na dare agogon Najeriya ake sa ran za a yi wasan karshe a G0asar Cin Kofin Afirka da ke gudana a Masar.

Za a yi wasan ne a tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Senegal da kuma takwararta ta Aljeriya.

Kamar yadda tarihi ya nuna, sau daya Aljeriya ta taba lashe wannan kofi inda ta dauka a 1990 bayan ta lallasa Najeriya da ci 1-0.  Ita kuma Senegal ba ta taba lashe wannan kofi ba. A 2002 ne ta buga wasan karshe da Kamaru amma Kamaru ta doke ta a bugun finareti bayan sun tashi wasan babu ci.

Kimanin shekara 29 ke nan rabon da Aljeriya ta lashe wannan kofi, yayin da Senegal kuma ta yi kimanin shekara 17 rabon da ta kai wasan karshe.

Masana harkar kwallon kafa suna ganin wasan zai yi zafi ganin dukkan kasashen biyu suna neman lashe wannan kofi don shiga kundin tarihi.

ADVERTISEMENT

Tuni zaratan ’yan wasa irin su Sadio Mane na Senegal da Riyad Mahrez na Aljeriya suka shirya tunkarar wannan wasa.

Daga yau kuma sai shekara 2021 za a sake yin irin wannan gasar a kasar da Hukumar CAF za ta sanar nan gaba.

Share