Da Dumi Dumi

Afirka ta Kudu ta shawo kan rikicin adawa da baki

Gwamantin Afirka ta Kudu ta kwantar da rikicin kiyayya ga baki, a wasu garuruwan kasar, inda ta yi nuni da cewa wadanda suka yi sace-sace a shagunan baki “’yan iska ne masu aikata ta’asa.”
Wadannan sace-sace da kassara dukiyar wadanda ba ’yan kasa ba, ta jefa mutane cikin dar-dar, don gudu kaga a sake kwata abin da ya auku a shekarar 2008, ionda aka tursasa baki suka yi ta barin kasar.
Mai magana da yawun gwamnati, Pumla Williams, ta ce : “Gwamnati ta lura tare da nuna damuwa kan yadda aka rika kai wa baki farmaki a wasu garuruwa da ke gefen birnin Johannesburg. Mun yi tur da wannan ta’annati da ak yi wa baki .
tare da wasu al’ummar kasar Afirka ta Kudu.” Masu ta’asar dai sun fi yin illa a garin Diepsloot, wani gari da ke Arewa da birnin Johannesburg. Shi kuwa wani dan kasuwa bako, ya bayyana wa ’yan sanda cewa, lokacin da wasu mutum biyu suka zo yi masa fashi, sai kawai ya bude musu wuta. Wadannan garuruwa da ke kewaye da birnin Johannesburg, al’ummominsu na fama da talauci ga rashin ayyukan yi.
Tuni aka tura jami’an ’yan sanda da motoci masu sulke don su tsare garin, musaman ganin yana da yawan shagunan kasuwanci na baki.