✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ahmed Bamalli ya zama Sarkin Zazzau na 19

Sarkin Zazzau

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya sanar da nadin Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin Sarkin Zazzau na 19.

Rahotanni da muke samu sun ce tuni sabon sarkin ya isa fadarsa bisa rakiyar Sakataren Gwamnain Jihar Kaduna, Balarabe Abbas Lawal.

Sanarwar da Gwaman ya fitar a ranar fitar a ranar Laraba ta ce nadin magajin Sarki Shehu Idris wanda ya rasu ranar 20 ga watan Satumba, 2020 ya fara aiki ne nan take.

Sarki Ahmed Bamalli shi ne Sarkin Zazzau na farko daga gidan sarautar Mallawa tun bayan rasuwar kakansa, Sarki Alu Dan Sidi shekara 100 da suka wuce.

Kafin nadinsa, shi ne Magajin Garin Zazzau, kuma Jakadan Najeriya ak kasa Thialand da kuma Myarnmar.

Sanarwar dauke da sa hannun Kwamishinan Kananan Hukumomi da Masarautu, Ja’afaru Ibrahim Sani, ta ce nan gaba gwamnatin jihar za ta sanar da shirye-shiryen mika wa sabon sarkin sandar mulki.

Gwamnatin Jihar ta yi wa sabon sarkin murna tare da addu’ar Allah Ya taya shi riko.