✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwai bukatar mu rika damawa da Ahlus Sunnah a gwamnati – Shugaban Iran

Shugaban Kasar Iran Hasan Rouhani ya ce akwai bukatar Ahlus Sunnah da al’ummar Turkmen su samu mukamai masu yawa a gwamnatinsa ta yadda za a…

Shugaban Kasar Iran Hasan Rouhani ya ce akwai bukatar Ahlus Sunnah da al’ummar Turkmen su samu mukamai masu yawa a gwamnatinsa ta yadda za a rika damawa da su a gwamnatance.

Rouhani ya ce Alhlus Sunnah sun dade suna matsa lamba ga gwamnatocin Iran a lokuta daban-daban don tabbatar da wannan kudiri na su ma sun samu damar rike madafun iko a kasar.

Shugaban na Iran ya bayyana haka ne a lokacin da ya ziyarci Jihar Gulistan, inda ya zanta da manema labarai har  ya tabo batun Ahlus Sunnah da Turkmen da ke kasarsa.

Shugaba Rouhani ya kara da cewa sun dauki lokaci mai tsawo suna son gwamnatocin Iran su tafi tare da mabiya mazhabobi daban-daban da kuma kabilu marasa rinjaye, inda ya ce akwai bukatar Ahlus Sunnah da kabilar Turkmen su samu mukamai da dama a gwamnati.

Ya ce “A wajenmu, Ahlus Sunnah da kabilar Turkmen ya zama dole su samu manyan mukamai a gwamnati da harkokin gudanarwa. Dole ne mu yi kokarin amfana da kwarewa da kaifin basira na ’yan kasarmu. A yankunan Kudanci da Arewacin kasarmu, ana ware wadansu mutane, yankin Turkmen na daga cikin wadanda aka ware tare da hana su shiga gwamnati.”

Rouhani ya ci gaba da cewa sun dauki matakai da yawa a matsayinsu na gwamnati, kuma a yanzu akwai Ahlus Sunnah da Turkmen da suka hada da mata da suke rike da mukaman jakadu, mataimakan gwamnanoni, daraktoci da sakatarorin kananan hukumomi, abin da ya bayyana a matsayin ci gaba.

Ya ce, akwai bukatar a kara zama a wannan bangare kuma wannan yunkuri wani bangare ne na alkawarin bai wa mata kashi 30 cikin 100 na mukaman gwamnatinsa.

A kwanakin baya gwamnatin Rouhani ta nada mace Ahlus Sunnah ta farko a matsayin jakadiyar Iran a kasar Brunei