✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwai yiwuwar Trump ya gana da Shugaban Iran

Shugaban Amurka Mista Donald Trump da takwaransa na Iran Hassan Rouhani za su halarci taron Majalisar Dinkin Duniya a New York a watan Satumban nan…

Shugaban Amurka Mista Donald Trump da takwaransa na Iran Hassan Rouhani za su halarci taron Majalisar Dinkin Duniya a New York a watan Satumban nan

Shugaban Iran, Hassan Rouhani ya bukaci Amurka ta fara cire wa kasar takunkumin da ta kakaba mata a matsayin matakan farko na neman tattaunawa da Iran. Yana mai cewa takunkumin da aka saka musu, “haramtattu ne kuma rashin adalci ne.”

Cikin wasu kalaman kai-tsaye da Rouhani ya gabatar ta gidan talabijin din kasar, ya ce dole ne Amurka ta janye haramtattun takunkumin da ta kakaba wa Iran wadanda Shugaban ke cewa su ne mafarin tattaunawarsu da kuma warware rikicinsu.

“Idan har ba a dauki matakin cire takunkumin ba, ba za a iya bude wannan dan mukulli ba,” inji Rouhani.

Rouhani ya fadi haka ne kwana guda bayan da Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce kofarsa a bude take domin tattaunawa da kasar Iran idan har akwai bukatar haka.

Rikici tsakanin Amurka da Iran dai ya ta’azzara bayan da Donald Trump ya fice daga yarjejeniyar takaita shirin nukiliyar Iran a bara, sannan ya sake kakaba wa Iran din jerin takunkumi.

Shugaba Donald Trump na son a sake yarjejeniyar da za ta taka wa Iran birki kwata-kwata kada ta ci gaba da shirin samar da nukiliya, batun da Iran ta ki amincewa da shi.

Sauran manyan kasashe da suke cikin yarjejeniyar ta 2015 wato Birtaniya da Faransa da Jamus da China da kuma Rasha sun yi kokarin ci gaba da mutuntata amma jerin takunkumin da Amurkar ta kakaba wa Iran ya janyo tabarbarewar tattalin arzikin kasar.

Kasashen duniya sun daina sayen man kasar Iran, sa’annan darajar kudinta ta karye baya ga tashin gwauron zabo da farashin kayayyaki ya yi.

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron a shafinsa na Twitter ya bayyana cewa shi da Donald Trump na Amurka sun yarda da cewa ya kamata a tattauna da Iran. Amma ba su amince da ci gaba da ayyukan samar da makaman nukiliya ba.

Me Donald Trump ya ce?

A ranar Litinin ne yayin wani jawabi ga manema labarai na hadin gwiwa a lokacin taron kasashe bakwai masu tattalin arzikin duniya a Biarritz, Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya ce ya fada wa Hassan Rouhani na Iran ta waya cewa “Ya gamsu cewa za a iya cimma matsaya,” idan har zai yarda ya hadu da Mista Trump.

“Abin da nake fata a makonni masu zuwa…za mu iya ganin yadda za mu gana.”

Mista Trump ya ce ganawar da za su yi ta gaskiya ce, inda ya kara da cewa Iran za ta samu rancen kudade daga kasashen duniya domin ta tayar da komadar tattalin arzikin da ta yi fama da shi.

“Ina ji a jikina cewa Rouhani zai so ya yi wannan ganawar domin fitar da kasarsa daga kangin da take ciki. Iran na fama da wahala.”

Taron ne zai zama wani wuri da Shugaban Amurka da na Iran za su hadu a karon farko tun 1979 lokacin da kasashen biyu suka samu rashin fahimta bayan juyin juya-halin kasar Iran.

Mene ne martanin Hassan Rouhani?

Ya ce, “Idan Amurka ba ta cire takunkumin ba kuma Shugaba Trump bai yi watsi da matakin da kasar take dauke ba, babu wata tattaunawar arziki da za mu cimma. Cimma wannan yarjejeniyar kacokan na hannun Amurka ne.”

Hassan Rouhani ya ce “Idan abin da ke bai wa Mista Trump tsoro shi ne batun shirin nukiliyar Iran, to ya sha kuruminsa.” A cewar Rouhani matukar Amurka ba ta dauki matakan warware rikicin ba, a shirye Iran take ta ci gaba da aikata abin da zai muzguna mata, musamman ta hanyar ci gaba da kokarin mallakar makamin nukiliya.

“Ba mu da burin mallakar makaman kare dangi ko makaman nukiliya, ba kuma mun ki mallaka ba ne saboda Amurka ba ta so ko kuma saboda gargadin da suke yi wa duniya, sai dai kawai saboda irin abin da muka yi imani da shi da kuma fatawar shugaban addininmu,” inji shi.

Shugaban addini na kasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya fitar da wata Fatawa a shekarar 2013 wadda ta yi watsi da mallakar makaman nukiliya.

To sai dai kasashen duniya ba su amince da cewa Iran din ba ta bukatar mallakar makaman nukiliya ba.

Kwana guda bayan taron G7, Shugaban Iran ya yi fatali da kalaman Mista Trump cewa Amurka na iya tattaunawa da kasarsa.

Abin da ya fito fili shi ne dole kasashen biyu – Amurka da Iran su kauce wa kara fadawa cikin wani sabon rikici. Kuma abu muhimmi shi ne shugabannin kasashen biyu su amince da wani mataki da za su iya nuna wa ’yan kasashensu a matsayin wata nasara komai kankantarta.

Ya ce ko a baya-bayan nan, Shugaba Trump ya bayyana yadda takunkumin ke tasiri a kan kasar Iran.

Shugaba Trump ya ce, takunkumin na cutar da su, ba na son ganin haka, ba zai yiwu mu bar su su mallaki makamin nukiliya ba, ba zai yiwu ba, lallai akwai yiwuwar za mu gana.