✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwai yiyuwar sake barkewar yaki tsakanin Isra’ila da Faladinawa

Sojojin Isra’ila sun kai wani hari na ba-saban ba ranar Talata a Zirin Gaza wanda ya yi sanadin kisan wani babban kwamandan wata kungiyar masu…

Sojojin Isra’ila sun kai wani hari na ba-saban ba ranar Talata a Zirin Gaza wanda ya yi sanadin kisan wani babban kwamandan wata kungiyar masu kishin addinin Musulunci mai suna Islamic Jihad.

Wata sanarwa daga ofishin Firayi Minista Benjamin Netanyahu ta ce Bahaa Abu el-Atta shi ne ya kai wasu hare-haren ta’addanci da yawa, da kuma harba wa Isra’ila rokoki a cikin ’yan watannin nan, kuma ya kudiri aniyar kai wasu hare-haren.

Jim kadan bayan sanar da kai farmakin ne, Kungiyar Islamic Jihad ta tabbatar da rasuwar babban kwamandanta a Gaza Baha Abu Al-Ata mai shekara 42, tare da mai dakinsa a gidansu da jiragen yakin Isra’ilar suka ragargaza, gami da hallaka wadansu mutum uku da jikkata wadansu 18, bayan haka ya raunata ’ya’yansu.

Kungiyar ta lashi takobin daukar fansa, kamar yadda kungiyar mayakan Hamas ita ma ta yi, wadda ta ce Isra’ila ce za ta fuskanci duk wani sakamakon da zai biyo baya a kan wannan mummunan farmaki da kuma yadda take kara auna su.

Tuni mayakan Falasdinawa suka mayar da martani a kan matakin da Isra’ila ta dauka ta hanyar harba mata rokoki, lamarin da ya haifar da fargabar barkewar sabon yaki a tsakanin bangarorin biyu.

Farmakin Isra’ila ya jawo zazzafan martani daga Falasdinawa, inda mayakan Islamic Jihad suka harba makaman roka 50 kan wasu yankunan Isra’ila ciki har da biranen Kudus da Tel Abib, sai dai rundunar sojin kasar ta ce ta yi nasarar kakkabo 20 daga cikin makaman, amma duk da haka mutum 29 sun jikkata.

Islamic Jihad ce Kungiyar mayakan Falasdinawa ta biyu mafi karfi a yankin Gaza bayan Hamas, wadda suka kulla yarjejeniyar kawance.

Yanzu dai Isra’ila ta girke dakarunta aiyakar yankin Gaza cikin shirin kaddamar da yaki ko kariya daga barazanar hare-haren mayakan Falasdinawa.