✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Allah Ya amshi ran mahaifiyar limamin Kubwa

Mahaifiyar Babban Limamin Masallacin Kubwa Abuja, Malam Abdulmumini Ahmad Khalid ta kwanta dama. Marigayiyar mai suna Hajiya Halima Khaild da ake kira da Dada ta…

Mahaifiyar Babban Limamin Masallacin Kubwa Abuja, Malam Abdulmumini Ahmad Khalid ta kwanta dama.

Marigayiyar mai suna Hajiya Halima Khaild da ake kira da Dada ta rasu ne a ranar Asabar da ta gabata, bayan gajeruwar rashin lafiya. Ta rasu tana da shekara 85 a duniya.

Hajiya Halima, wadda ’yar asalin Jihar Sakkwato ce, ta yi karatun addini da na boko a bangaren ilimin jinya, sannan ta yi aikin koyarwa ga matan aure, inda ta bude makaranta a garin Mubi da ke Jihar Adamawa kafin ta ci gaba da aikin a Kano na wani lokaci.

Daga baya ta dawo Abuja kamar shekara 10 da suka gabata, inda ta mai da hankali a bangaren karatu da ayyukan addini. Ta rasu ta bar ’ya’ya 12 da jikoki da tattaba kunne 83, kamar yadda aka tabbatar wa Aminiya.

Daga cikin wadanda suka kai gaisuwar ta’aziyya ga iyalan marigayiyar akwai Babban Limamin Masallacin Abu Zarril Gifari da ke Unguwar Garki Abuja, Malam AbdurRahman Al-Zamfari wanda kuma shi ne ya jagoranci yi mata Sallar Jana’iza a Masallacin Badar da ke Kubwa. Sauran sun hada da Malam Abdul-Jalil Dabo na masallacin Usman bin Affan sai kuma Sheikh Tajuddin Bello na masallacin Zone 3 da sauran limamai daga yankuna daban-daban na Abuja.

Shugaban karamar Hukumar Bwari, Mista Musa Dikko da Kansilan Kubwa Ali Dogo da tsohon Babban Daraktan Hukumar Wutar Lantarki ta kasa, Alhaji Shu’aibu Maigida suna cikin wadanda suka kai gaisuwar ta’aziyyar rashin.

Babban danta, Malam Abdulmumini Ahmad Khalid na daya daga cikin limamai da ke ba aiko da hudubobi ga jaridar Aminiya.