✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Allah Ya yi wa diyar Shaikh Pantami rasuwa

Allah Ya yi wa diyar Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Shaikh Isa Ali Pantami mai suna Aishah (Amal) rasuwa. Ministan ya sanar da rasuwar…

Allah Ya yi wa diyar Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Shaikh Isa Ali Pantami mai suna Aishah (Amal) rasuwa.

Ministan ya sanar da rasuwar a shafinsa na sada zumunta a ranar Litnin.

“Inna lil Laahi wa inna ilaiHi Rajiun! A yanzu Allah (SWT) Ya dauki rayuwar ‘ya ta, wato Aishah Isa Ali (Amal) mai shekaru kusan goma sha uku da haihuwa,..”, inji shi

Shaikh Pantami ya kuma sanar cewa za a yi janar Aisha Amal ranar Talata a  Masallacin Annur da ke Abuja bayan sallar Azahar.

“Saboda wasu uzururruka, janaza sai gobe (Talata) a Masallacin Annur bayan Sallar Azahar, karfe 1:15pm”, kamar yadda ya sanar.

Allah Ya jikanta, Ya gafarta mata, Ya kyauta tamu zuwar.