✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Allah Ya yi wa matar Farfesa Yadudu rasuwa

Ta rasu a wani asibiti da ke Kasar Amurka.

Allah Ya yi wa Hajiya Zainab Auwalu Yadudu rasuwa, matar fitaccen Farfesan na Shari’ah kuma tsohon mashawarci ga Shugaban Najeriya a zamanin mulkin soji, Janar Sani Abacha.

Farfesa Auwalu Yadudu wanda tsohon Shugaban Tsangayar Shari’a ne na Jami’ar Bayero da ke Kano, ya aike da sakon rasuwar mai dakinsa daga Kasar Amurka a ranar Lahadi.

Ya ce marigayiya Hajiya Zainab, wadda suka kwashe sama da shekara 40 tare, ta rasu ne a asibiti bayan ta cika kalmar Shahada.

Ya kara da cewa ana shirin maido gawarta Najeriya domin yi mata jana’iza.

“Allahu Akbar, yanzu na samu sako daga Farfesa Auwalu Yadudu daga Kasar Amurka, inda ya bayyana bakin cikin rasuwar matarsa ​​da suka shafe sama da shekara 40.

“Daga Allah muke kuma gare shi za mu koma. AlhamdulilLah, Zainab Auwalu Yadudu ta rasu da kalmar Shahada a bakinta a yau 8 ga watan Janairu 2023 a Asibitin Jami’ar Kentucky da ke Kasar Amurka da misalin karfe 12:52 na rana.

“Muna shirye-shiryen kawo gawarta Najeriya domin yi mata jana’iza kuma za mu bayyana karin bayani nan gaba, in sha Allahu.”