✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliya: Fursunoni 228 sun tsere daga gidan yari a jihar Kogi

Fursunoni 228 sun tsere daga gidan yarin garin Koton Karfe na jihar Kogi. Majiyarmu ta samu rahoton cewa, Fursunonin sun tsere bayan ambaliyar ruwa ta…

Fursunoni 228 sun tsere daga gidan yarin garin Koton Karfe na jihar Kogi. Majiyarmu ta samu rahoton cewa, Fursunonin sun tsere bayan ambaliyar ruwa ta rusa wani bangare na ginin gidan yarin.

An dai fara ruwan saman kamar da bakin kwarya da kamar misalign karfe 2 na tsakar daren yau Litinin.

Mai ba gwamnan jihar Kogi a fannin tsaro, Jerry Omodara (mai ritaya) ya ce a yanzu haka an kama fursunoni 100 cikin wadanda suka tsere