✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliya: Sama da mutum 50,000 sun rasa muhallansu a Kogi

Ambaliyar ruwa daga Kogin Neja ta shafi akalla gundumomi 70 da kuma raba sama da mutum 50,000 da muhallansu a sassa daban-daban na jihar Kogi.…

Ambaliyar ruwa daga Kogin Neja ta shafi akalla gundumomi 70 da kuma raba sama da mutum 50,000 da muhallansu a sassa daban-daban na jihar Kogi.

Mazauna yankunan a yayin wata tattaunawa da Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) da takwararta ta Jihar Kogi (KOSEMA) sun koka cewa ambaliyar ta fara kamari ne cikin kwanaki biyar din da suka gabata.

Daya daga cikin mazauna yankunan, Ibrahim Abdullahi wanda kuma shi ne jami’in da ke kula da harkar muhalli da bayar da agajin gaggawa a Karamar Hukumar Kogi ya ce yankuna 66 ne ambaliyar ta shafe a jihar.

Ibrahim ya kuma ce lamarin ya tilsata wa sama da mutum 50,000 yin kaura daga gidajensu inda a yanzu suke neman mafaka a makarantu, gidajen mai da sauran muhimman wurare.

Ya ce wasu daga cikin wadanda lamarin ya shafa a Edeha da Koton Karfe sun rika kwana a kan tituna inda suke artabu da sauro da ragowar muggan kwari.

Ibrahim ya ce hakan ya sa ala tilas makarantu a yankunan suka rufe a inda aka mayar da su sansanonin wadanda iftila’in ya raba da muhallansu.

Daga nan ya yi kira ga gwamnatin jihar da hukumar NEMA kan su kawo musu dauki.

Kazalika, Shugaban Kawamitin Kula da Ambaliya na Karamar Hukumar Ibaji, Mista Omonu James ya ce dukkannin makarantu 26 da ke karamar hukumar yanzu sun koma mafaka ga wadanda ambaliya ta yi wa barna.

Ya ce har asarar rai sai da aka samu a yankin, yana mai gargadin cewa akwai yiwuwar samun karin wasu mace-macen matukar ba a daukin matakan da suka kamata ba.

A yayin taron dai gwamnan jihar, Yahaya Bello ya ce sun ware kudade masu yawa  domin sayen magunguna, abinci, ruwa da sauran kayan tallafi ga mutanen da ambaliyar ta shafa.

Bello, wanda mataimakinsa Edward Onoja ya wakilta ya ce tuni ya umarci a debo matasa 21,000 daga cikin wadanda Gwamnatin Tarayya ta diba domin ayyukan raya kasa don su taimaka wajen ceto.