✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliya ta ci mutum 5 da rabin gari a Jigawa

Ambaliyar ta mamaye rabin garin Miga da kuma wasu garuruwa a a yankin

Ambaliyar ruwa ta lalata kusan rabin garin Miga, hedikwatar Karamar Hukumar Miga ta Jihar Jigawa bayan an shafe kusan kwana uku ana ruwan sama ba kakkautawa.

Iftila’in ya kuma shafi wasu yankunan Karamar Hukumar tare da yin sanadiyyar rasuwar akalla mutum biyar da kuma lalata gidaje da dama.

Wuraren da lamarin ya fi yi wa ta’adi sun hada da Sakatariyar Karamar Hukumar, gidajen matasa masu yi wa kasa hidima, babban asibitin garin, ofishin ’yan sanda da kuma gidan hakimi.

Yayin da ya ke zagayawa da ’yan jarida wuraren da ambaliyar ta shafa, Shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Mohammed Abubakar Agufa ya ce mutanen na matukar bukatar tallafi daga gwamnatin jihar da ta tarayya.

Ya ce sauran yankunan da lamarin ya shafa sun hada da Hantsu, Sabongari, Tsokuwawa, wani sashe na Dangyantum, Sansani, Koya da kuma Yanduna.

Ko da yake bai bayar da cikakkun alkaluman gidajen da suka lalace ba, Shugaban Karamar Hukumar ya ce ya zuwa yanzu an tabbatar da rasuwar mutum biyar, ciki har da wani yaro mai rarrafe wanda yanzu haka kakarsa ke kwance a gadon asibiti sakamakon karayar da ta samu a kafafu.

A cewarsa, duk da yake ba a kai ga samun tallafi daga Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ba, takwararta ta jihar (SEMA) ta tallafa musu da buhunan garin rogo guda 70, na kuli-kuli guda 50 sai kuma na sukari guda 30.

Kazalika hukumar ta ba su kwalekwale guda daya wanda za a yi amfani da shi wajen jigilar kayan tallafin.

Daga nan sai ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta kammala aikin yashe kogin Hadeja wanda ya fara tun daga Ringim har ya dangana da garin Guri.

Ya ce muddin aka kammala aikin, to zai kawo karshen matsalar ambaliyar ruwan da ake fuskanta a yankin kusan a kowacce shekara.