✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliyar ruwa a Madagascar: Ana fargabar yunwa da tamowa

Akalla mutum dubu 16 ne suka rasa muhallansu bayan saukar wani mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya a yankuna bakwai na kasar Madagascar cikin…

Akalla mutum dubu 16 ne suka rasa muhallansu bayan saukar wani mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya a yankuna bakwai na kasar Madagascar cikin kwanakin da suka wuce.

Ruwan sama mai karfin gaske hade da zabtarewar kasa ya haddasa salwantar rayuka mutane fiye da 30 bayan mako guda ana tafka ruwan sama babu kakkauta wa.

Garin Marovoay da ke Arewa maso Gabas na kasar na cikin inda ambaliyar ruwan ta mamaye, inda lamarin ya haddasa yin hijirar dubban jama’a daga gidajensu.