✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 18 da tarwatsa 41,000 a Neja

Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Neja (NSEMA) ta sanar da cewa, ambaliyar ruwa da aka yi a jihar a wannan shekarar 2019 kimanin mutum…

Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Neja (NSEMA) ta sanar da cewa, ambaliyar ruwa da aka yi a jihar a wannan shekarar 2019 kimanin mutum 18 ne suka mutu yayin da ambaliyar ta tarwatsa mutum dubu 41 da 959 daga gidajen su.

Darakta Janar na Hukumar NSEMA Alhaji Ahmed Inga, ne ya sanar da hakan a  Minna babban birnin jihar lokacin da hukumar ta sanar da abin da ambaliyar ta haddasa tare da hadin giwar Kwamitin bada agajin gaggawa na Karamar Hukuma.

Alhaji Ahmed, ya kara da cewa, ambaliyar ruwan ta afkawa kananan hukumomi 20 da unguwanni 516 da wasu yankunan unguwanni 152, yayin da gidaje dubu 2,714 suka rushe sannan ambaliyar ta yi sanadiyyar tarwatsa mutum dubu 41,959.

Kananan hukumomin da ambaliyar ta shafa sun hada da: Mokwa, Lapai, Lavun, Borgu, Shiroro, Katcha, Kotangora, Mashegu, Gurara, Suleja, Gbako, Chanchaga, Bosso, Agaie, Agwara, Rafi, Munya, Edati, Paikoro da karamar hukumar Wushishi.