✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

“Aminan Juna”

Assalamu alaikum Manyan gobe tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labari ne a kan “Aminan juna”. Labarin…

Assalamu alaikum Manyan gobe tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labari ne a kan “Aminan juna”. Labarin ya yi nuni da yadda aboki nagari ke gane matsalar abokinsa ba tare da ya fada masa ba. A sha karatu lafiya.

 

Malam Hamidu da Malam Shehu aminan juna ne tun suna yara. Sai dai Malam Hamidu ya fito ne daga gidan sarauta.

Bayan shekaru masu yawa, sai Allah Ya yi wa mahaifin Malam Hamidu rasuwa. Da ma Malam Hamidu shi ne kadai da a wajen mahaifinsa. Hakan ya sanya aka nada shi sarauta.

Shi ko Malam Shehu rayuwa ta yi masa tsanani yana fama da talauci hatta abincin da zai ciyar da iyalinsa yana gagararsa har sai ya fita roko a makwabta.

Matarsa ta ba shi shawarar ya kai ziyara wajen Sarki Hamidu tun da sun yi amintaka a lokacin da suke yara ko za a dace.

Ta shiga makwabta ta roko shinkafa ta yi waina ta zuba a kwano ta bai wa maigidanta ya kai wa Sarki Hamidu.

Malam Shehu na isa fada sai dogarai suka tsayar da shi. Ganin yadda kayan jikinsa a yage sai ya roki alfarma da su fada wa Sarki cewa amininsa ne Malam Shehu ya kawo masa ziyara.

Sako na isa sai aka ga Sarki ya fito da kafarsa inda ya yi wa Malam Shehu maraba.

Da Malam Shehu ya ga irin tarbar da Sarki ya yi masa, sai ya ki fada wa Sarkin irin halin kuncin rayuwar da yake ciki.

Bayan sun gaisa da Sarki sai Malam Shehu ya koma gida.  Amma abin mamaki isar gida ke da wuya sai ya ga an canza fasalin gidan da kayan alatu.  Da ya tambayi matarsa sai ta ce Sarki ne ya aiko aka yi musu goma-ta-arziki.

Tare da fatan Manyan gobe za su rika taimakawa abokansu a nan gaba idan sun ga suna da bukata ba sai an tambayesu ba.