✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Aminu Ado Bayero ya zama sabon Sarkin Kano

Sakataren gwamnatin jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji ne ya sanar da cewa, gwamnatin jihar Kano a ranar Litinin, jim kadan bayan tube Sarki Sanusi II,…

Sakataren gwamnatin jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji ne ya sanar da cewa, gwamnatin jihar Kano a ranar Litinin, jim kadan bayan tube Sarki Sanusi II, ta nada Aminu Ado Bayero a matsayin sabon Sarkin Kano.

Kafin nadin nasa shi ne sarkin sabuwar masarautar Bichi, kuma daya daga cikin hudu na sabbin Masarautu da Gwamna Ganduje ya kirkira a shekarar 2019.

Aminu Ado Bayero wanda da ne ga marigayi Sarki Ado Bayero, hakan yasa ya zama sarki na 15 a jerin Sarakunan Fulani na Kano.