✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin tambayoyi

Wadanne alamomi mace za ta gani idan tana da ciwon daji na mama? Daga Zainab Ishak Amsa: A mafi yawan lokuta ciwon sankarar mama da…

Wadanne alamomi mace za ta gani idan tana da ciwon daji na mama?

Daga Zainab Ishak

Amsa: A mafi yawan lokuta ciwon sankarar mama da kullutu yake farawa a jikin mama, kafin kullutun ya rikide ya zama daji. Don haka duk macen da ta ji wani kullutu a mamanta wanda ya yi kwanaki da dama ya ki tafiya, kuma ba wai yana da alaka da al’ada ba (tun da akwai wasu kumburin da suke da alaka da al’ada), to dole a je a duba shi, watakila ma a yanke shi a kai dakin bincike a tabbatar ba daji ba ne.

Sauran alamu wadanda ba a cika gani ba su ne na canjin yanayin fatar maman kamar tattarewa, ko canjin kalar fatar maman, ko zubar wani ruwa, ko yawan zafi ko zogi daga ciki ko daga kan maman haka kawai.

A mafi yawan lokuta, wadannan alamu musamman ma kullutun zai dade a jiki ba a san ma akwai ba, har ya zo ya zama daji. Shi ya sa ake son yawan duba mama a gaban madubi da laluben kullutu a jikin mama duk bayan ’yan watanni domin a ji ko daidai suke ko kuma a’a.

 

A lokacin al’adana jini na zuba sosai. Ko hakan matsala ce?

Daga Hafsat A. Bauchi

Amsa: E, zubar jini da yawa lokacin al’ada matsala ce da sai kin je an duba dalili, domin mun sha zayyano cututtukan da kan jawo wannan. Wato ke nan ma ce ba za ta rika zubar jini da yawan duk wata ba ba tare da wani dalili kwakkwara ba. Idan kika je asibiti aka yi maki ’yan tambayoyi da ’yan dube-dube, za a iya gano inda matsalar take.

 

Zan iya yi wa yarona dan watanni takwas shayi a yanzu?

Daga Murjana Dabai

Amsa: E, za ki iya. A da kamar kina bin wannan shafi sosai, domin an yi wannan bayani a baya inda aka ce tun daga haihuwa har shekaru shida ko bakwai duk lokacin da iyaye ke so. Kuma an fi so a lokutan sanyi saboda karancin kwayoyin cuta irinsu bacteria masu hawa ciwo.