✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin tambayoyi daban-daban

Ni ne dai hakorana guda uku suka zube a lokaci guda ga shi ko shekara talatin ban kai ba. Ina tauna abinci kamar tsoho. Ko…

Ni ne dai hakorana guda uku suka zube a lokaci guda ga shi ko shekara talatin ban kai ba. Ina tauna abinci kamar tsoho. Ko akwai wani taimako da za a iya mini?

Daga Aminu Muhammad

Amsa: Eh, akwai yadda za a yi mana, ba ka san ana dashen hakora ba? Asa na tangaran a bi su da noti a daure? Kamar yadda akan daure kashin da ya karye. Sai dai ban sani ba ko wannan fasaha ta zo nan Najeriya zuwa yanzu.

Me ke sa hakora karairayewa suna cirewa ne?

Daga Zaiyanu Kokiya

Amsa: Rashin kula da su ne kan kawo haka. Rashin kula da su ya hada da rashin tsabtace su da makilin ko asuwaki da cin abinci masu kara musu kwari kamar madara da kifi masu sinadarin calcium mai kara kwarin kashi da hakora.

Shin da gaske ne cin abinci mai zafi zai iya kawo matsala ga jiki?

Daga Muhammad Adamu Garun-Gabas

Amsa: A’a a likitance cin abinci mai zafi sai dai ya kona baki ko harshe amma ba ya kawo wata matsala ta sauran sassan jiki. Akwai dai bincike da ya tabbatar da cewa yawan cin gasasshen abu kamar nama ko kifi wanda ya fara konewa zai iya jawo ciwon dajin makoshi, wato wannan baki-bakin da ke nuna kuna zai iya sa ciwon daji in ana cinsa na tsawon lokaci.

Idan ina wurin aiki sai in rika samun ciwon kai a-kai-a-kai. Ina yawan shan magani panadol amma ina tsoron kada ya yi mini illa. Ko ba matsala in rika shan maganin? Kuma aikin nawa a rana nake.

Daga Dan Kurma, Zariya

Amsa: Eh, ga alama yawan ciwon kan naka ya ta’allaka ne a kan yawan shiga rana. To shi wurin da kake aikin ba ka iya sa masa rumfa? Idan kuma ba za ta yiwu ba, kamar idan aikin na zirga-zirga ne ai za ka iya sayen malafa ko ka sa a hada maka hular lema. Amma maganar shan maganin ciwon kai a kullum ba mafita ba ce.

Idan ina karanta littafi kuma ya zamo wurin da sanyi kamar na AC ko akwai hayaki sai in ji idanuna sun kama zafi da hawaye. Ko me ke kawo haka?

Daga Aminu Gambo, Kaduna

Amsa: Ko da hayaki a wuri, ko da sanyi, kai ko ma mene ne, idan mutum ya fara jin zafi da hawaye yayin karatu mukan ba shi shawara ya ziyarci wurin awon idanu a ga karfinsu ko sun fara rauni ko kuma a’a.

Ka yi magana a kan ciwon mimmikewar hannaye. Idan abin ya faru ga mutum matsalar za ta iya tafiya gaba daya? Domin na ji ka ce karancin sinadarai irin su calcium da na magnesium ne ke kawo shi.

Daga Kabir Ibrahim Matazu

Amsa: Eh, haka ne, mimmikewar hannaye sanadiyar karancin wasu sinadarai na jini yana warkewa sarai. Cikin kankanen lokaci da ba wa mai wannan matsala sinadaran da suka yi karanci za a ga sun dawo yadda suke.

Duk lokacin da aka yi ruwan sama sai fitsari ya dame ni. Ko ina da matsala ke nan? Shekaruna sun kai 58

Daga Mustapha H. Kano

Amsa: Ya danganta da abin da aka ce kana da shi a asibiti, tunda kai ka sha tambaya a nan a kan abin da ya shafi mafitsara. Zuwa yanzu ya kamata a ce kana da likita a asibitin mafitsara. Idan kuma ka je an ce ba ka da komai ke nan ba matsala ba ce.

Sana’ata ta zama ce. To sai na zo na samu ciwon kafa. Na je asibiti an yi mini aune-aune da gwaje-gwaje an ba ni magunguna na sha amma ba ta daina ba. Na koma amma ban samu likitan ba sai wani. Shin yaya ake bibiyar abin ne?

Daga Kabiru Maikaya, Sanga

Amsa: To ka ji illar yawan zama Malam Kabiru. Zama wuri daya na tsawon lokaci zai iya kawo irin wannan. Amma tunda ka ce an yi aune-aune da gwaje-gwaje da sauki, sai dai kawai watakila ba ka tambayi sunan ciwon kafar ba. Ko watakila ba a gano takamaimiyar matsalar ba. In dai ba a gano ba haka nan za ka daure ka yi ta bibiya har sai an dace an samu gano matsalar an magance ta. Wasunsu fa amma kamar ciwon sanyin kashi babu maganin waraka a likitance sai dai mai sa matsalar ta lafa, ya rika tashi jefi-jefi.

An ce garin-kwaki na illa ga ido. To idan an sarrafa fa zuwa teba da apu da sauransu?

Daga Adamu Ahmad Kwantagora

Amsa: Eh, ai ana ganin kamar illar tasa saboda sinadarin gubar cyanide ne, wadda ake ganin cewa idan an dafa garin tana raguwa. Don haka ke nan idan aka dafa kwakin aka sarrafa shi kamar yadda ka ambata, tabbasa akan rage yawan gubar.

Mece ce gaskiyar cewa shan itatuwan gargajiya masu daci zai iya kawo matsala ga jikin dan Adam?

Daga Muhammad Adamu Garun-Gabas

Amsa: Haka ne gaskiya saboda dacin zai iya zama guba. Shi maganin nasara ko da daga itaciya aka yi shi sai an tace gubar ta dawo daidai yadda ba za ta yi illa ga wani sashe na jiki ba.

Mene ne ke yawan jawo maiko da wani farin abu a fuska?

Daga Jamilu Ya’u, Kazaure

Amsa: Abin da ke kawo maiko shi ne maiko. Wato yawan cin maiko shi ke kawo maiko a fuska. Har farin abin duk maiko ne da ya daskare ya zama kamar kakide. Duk da cewa dai ba kowane mai cin maiko sosai maikon ke taruwar masa a fuska ba. Za ka iya ganin wadansu sun fi ka cin maiko amma ba ya nunawa a fatar fuskarsu watakila sai a ciki ko cinyoyi da damtse da sauransu. Za ka ga wadansu ma kwata-kwata kamar ba sa ci, babu alamar tara kitse a jikinsu saboda jikinsu nan da nan yake kone shi. Rage cin maiko zai taimaka wajen rage shi a fuska. Yawan wanke ta da sabulu kuma zai rage nason da maikon kan yi.