✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amurka ba ta da ikon kakaba wa Iran takunkumi —China

Kasar China ta kalubalanci sabon yunkurin Amurka na kara kakaba wa Iran takunkumin tattalin arziki. A shekarar 2015, tsohon shugaban kasar Amurka, Barack Obama, ya…

Kasar China ta kalubalanci sabon yunkurin Amurka na kara kakaba wa Iran takunkumin tattalin arziki.

A shekarar 2015, tsohon shugaban kasar Amurka, Barack Obama, ya cire takunkumin da aka sanya wa Iran sakamakon yarjejeniyar da suka cimma ta barin kera makami mai lizzami.

A hirarsa da ‘yan jarida, Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen China, Zhao Lijian, ya ce, “China na kalubantar takunkuman tattalin arziki da Amurka kadai ke son kakabawa, ko abin da ta kira hana kirar makamai”.

Zhao, ya kuma yi kira ga Amurka da ta yi biyayya ga matsayar da aka cimma a taron Kwamitin Tsaro na Duniya (Security Councli).

Ya ce, Amurka ba ta hurumin kara sanya wa Iran takunkumin tun da ta riga ta cire mata shi lokacin yarjejeniyar barin kirar makaman kare dangi da suka yi a lokacin mulki Obama.

Sai dai kuma kokarin gwamnatin Trump na kasashen duniya su ba da kai wajen sanya wa Iran takunkumin bai samu goyon bayan kasashe da yawa ba.

Har kawayen Amurka na asali, kamar su Birtaniya da Faransa ba su amince da kudirin na Amurka goyon baya ba, a taron kwamitin tsaro na duniya. Sai dai aka samu kasa daya da ta goya mata baya.