✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amurka ba za ta kasa biyan bashinta ba – Wanda ya ci kyautar Nobel

daya daga cikin masanan tsimi da tanadi na jami’o’in Amurka da ya ci kyautarNobel, Robert Shiller, ya bayyana cewa Amurka ba za ta kasa biyan…

daya daga cikin masanan tsimi da tanadi na jami’o’in Amurka da ya ci kyautarNobel, Robert Shiller, ya bayyana cewa Amurka ba za ta kasa biyan bashinta ba. Wannan farfesan tsimi da tanadi a Jami’ar Yale, yace yana cikin wanda aka sanar da shi cewa ya ci kyautar lambar yabo ta Nobel
“Ina gudun rashin jin sakon da aka bugo mini, don haka bna dauki waya tun cikin bandaki,’ a cewarsa, “wannan al’amari yana da ban mamaki, a hakikanin gaskiya ban zata ba.”
Cibiyar Royal Swedish Academy ta nazarin ilimin kimiyya, ta bayyana cewa Shiller da Eugene Fama da Lars Peter Hansen, wadanda farfesoshi ne a jami’ar Chigaco, sun samu nasarar samun lambar yabon ne kan wani nazarin bincike da suka gudanar kan yadda harkokin kasuwanni ke gudana.
Mutanen uku, sun share fage” kan fahimtar yadda farashin kadarori ke kasancewa. Da farko sun yi nazarin hawa da saukar farashi da asarar da ke tattare da harkar, a wani bagiren kuwa, sun yi nazarin dabi’un mutanen wajen kokarin kaucewa cijewar kasuwa,” a cewar Cibiyar Swedish Academy of Science. Shiller dan shekara 67 Farfesa ne a Jami’ar Yale, Fama dan shekara 74 da Hansen dan shekara 61 duk suna tare da jami’ar Chicago
Wannan lambar yabo da aka ba su, an danganta ta ne da nazarin da suka kan kimar darajar kadarori, wadanda suka hada da hannayen jari da kullin dukiyarna bashi mai riba (bonds), inda binciken nasu yayi daidai lokacin da tattalin arzikin duniya ke murmurewa daga durkushewar harkokin kasuwanci a tsawon shekaru 10 da suka gabata. Wadannan mutane uku an ba su “lambar yabo mai ban mamaki da jefa shakku” domin sakamakon bincikensu na nuni da cewa farashin hannayen jari da na kullin dukiya da sauran kadarori na da saukin yin hasashe na dogon lokaci, fiye da takaitaccen wa’adi na wucin gadi.
Fama da Hansen da Shiller za su raba kudin da kimarsu ta kai Kronor miliyan takwas, wato daidai da Dala miliyan daya da dubu 200, daidai da Naira biliyan biyu da miliyan 400
Shiller dai ya bayyana sunayen masana 22 da ya yi amfani da aikinsu na nazari, wajen gudanar da bincikensa, sannan ya yi godiya ga jami’ar da kuma tsangayar da yake yi wa aiki. “Har yanzu ina cikin tababa. Hakika an karramani a wannan taro. Yhar yanzu ina cike da mamaki yadda zan ci gaba zama a kan kimar da mutane suka dora ni a yanzu.” Inji shi.
“Ina ganin sauran aikin da ya kamata mu yi, don taimaka wa al’umma,” acewar shiller. Shiller ya kara da cewa sarrafa kudi al’amari da ake yi wa gurguwar fahimta, inda ake dora shi a gurbin takawa don zama mai kudui, alhali kuwa al’am,ari mne da ya shafi harkokin al’umma da dama, don wadata kansu abubuwan bukatu.