Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Amurka na shirin sake zama teburin sulhu da Taliban

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce manzonta a tattaunawa da kungiyar Taliban zai sake bude wata sabuwar tattaunawa da ‘yan gwagwarmayar Taliban cikin wannan watan na Yuni, a kasar Katar, a wani kokarin rattaba hannu a kan yarjejeniyar da za ta kawo karshen yaki mafi tsawon lokaci da Amurkar ta shiga.

Zalmay Khalilzad, wanda kwararren jami’in diflomasiya ne, wanda kuma shi ne yake jagorantar yunkurin cin ma yarjejeniyar wanzar da zaman lafiya da ‘yan Taliban, ya bar Amurka a karshen mako a wani rangadin kwanaki 17 da zai kai shi kasashen Afghanistan da Pakistan da Jamus da Belgium da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa, kamar dai yadda Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar ya sanar.

ADVERTISEMENT

Cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Wajen Amurkar ta fitar, ta fadi cewa a birnin Doha jami’in diflomasiyar zai sake komewa kan tattaunawa da kungiyar Taliban din, da nufin ciyar da yunkurin wanzar da zaman lafiyar gaba, bayan hutun kimanin wata guda da dakatar da tattaunawar.

A watannin da suka wuce, Mista Khalilzad ya gudanar da zaman tattaunawa da Taliban har sau shida, a kokarinsa na ganin ya cimma yarjejeniyar da a karkashinta Amurkar za ta janye dakarunta na farko da ta jibge a kasar Afghanistan, tun bayan hare-haren 11 ga watan Satumbar 2001.

ADVERTISEMENT

An dai yi imanin cewa, Amurka da Taliban sun amince da babban jigon bukatar mahukuntan birnin Washington tun daga shekarar 2001 da kuma a yanzu-wanda a ciki ake bukatar ’yan Taliban din da ka da su sake masu tsaurin ra’ayi su sake samun damar mayar da Afghanistan mafakarsu.

Sai dai babban abin da ake kiki-kaka a kai shi ne na rashin yadda daga bangaren Taliban da su zauna teburin sulhu da gwamnatin shugaba Ashraf Gani, da ke samun goyon bayan kasashen duniya.

Kungiyar Taliban wadda ta yi Imani da izzarta ta fuskar karfin soji, ta kuma yi watsi da bukatar tsagaita wuta a duk fadin kasar da shugaba Ashraf Gani ya yi ma ta tayi.

Cikin wani sakon da ba kasafai ya ke fitarwa ba, shugaban kungiyar Taliban a karshen makon jiya, Haibatullah Akhundzada, ya fadi cewa: “Bai kamata wani ya yi tsammanin mu ajiye makamanmu a fagen daga, ko kuma mu manta gwagwarmayarmu da kuma sadaukarwarmu na shekara 40, gabanin mu cimma muradunmu ba.”

A birnin Kabul, Zalmay Khalilzad zai gana da wakilan kungiyoyin fararen hula da na kare hakkokin mata, batun da ake da damuwa sosai game da ayyukan ‘yan Taliban.

Mista Khalilzad: “Zai kuma karfafa wa dukkanin bangarorin gwuiwa da nufin sulhu a tsakanin ‘yan kasar, wanda ake ganin zai haifar da sasantawa na karshe dan wanzar da zaman lafiya.” Inji ma’aikatar harkokin wajen Amurkar.

Jamus, wacce ita ma Mista Khalilzad zai yada zango a kasar, ta nuna soyayyarta wajen kiran taron samar da zaman lafiya a Afghanistan.

Jami’in diflomasiyar Amurkar, ya fara yada zango ne a kasar Pakistan, wadda itace ta ke kan gaba wajen marawa ’yan Taliban baya gabanin hare-haren 11 ga watan satumba, ta kuma yi amfani da sanayyarta ga Taliban din wajen taimakawa a zaman sulhun da ake yi da Taliban din.