Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Amurka ta yi Allah wadai da cin zarafin masu zanga zanga a Sudan

Masu zanga-zanga a Sudan
Masu zanga-zanga a Sudan

Sabuwar zanga-zangar da ta sake barkewa a birnin Khartuom na kasar Sudan inda akalla aka kashe mutum 11 ta samu suka daga gwamnatin Amurka.

Masu zanga-zangar suna neman a koma ga mulkin farar hula ne a kasar, maimakon na soji.

ADVERTISEMENT

’Yan sanda sun harba barkonon tsohuwa ga dubban masu zanga-zangar da suka taru a kan tituna ranar Lahadin da ta gabata a Khartoum, babban birnin kasar da kuma wasu yankunan don yin wannan zanga-zangar wadda ita ce ta farko tun wadda aka yi a watan Yuni da aka samu mace-macen mutane yayin murkushe ta.

Amurka ta yi Allah wadai da irin harin da jami’an tsaro suke  kai wa fararen hula masu zanga-zanga a kasar. A cewar Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka “Jami’an tsaron Sudan sun hallaka jama’a da yawa da suke zanga-zangar lumana, ya kuma kamata a kama su da laifin kisan da su ka yi wa fararen hula.”

ADVERTISEMENT