✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ba Messi damar barin kulob din Barcelona

Shugaban kulob din FC Barcelona da ke Sifen Jose Maria Bartomeu ya ce Lionel Messi yana da damar ya bar kulob din a karshen kaka…

Shugaban kulob din FC Barcelona da ke Sifen Jose Maria Bartomeu ya ce Lionel Messi yana da damar ya bar kulob din a karshen kaka ta bana muddin yana bukatar haka.

Shugaban ya bayyana haka ne a kafar sadarwarsa ta Twitter a ranar Litinin da ta gabata.

Lionel Messi wanda yake da kwantaragi da kulob din Barcelona har zuwa karshen kakar wasa ta 2021, a yarjejeniyar da ya kulla da kulob din ya nuna zai iya barin kulob din a karshen kakar wasa ta bana.

Rahotanni sun ce Messi dai ya ki sabunta kwantaraginsa da kulob din ne lokacin da kulob din ya nemi haka wanda haka ya sa wadansu ke hasashen zai iya barin kulob din a karshen kaka.

Sai dai mahukunta kulob din sun fara shiga wani hali ganin idan Messi ya bar kulob din da wuya ne su samu wanda zai iya maye gurbinsa.

Ya shafe fiye da shekara 10 yana buga wa kulob din kwallo inda ya samu nasarar lashe kofunan La-Liga 7 da na Zakarun Turai  uku da sauran kofuna.

Rahotanni sun ce idan Messi ya bar Barcelona watakila ya koma Amurka ko kasar haihuwarsa Ajantina don ci gaba da kwallo.