✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An bayar da umarnin kama shugaban kungiyar Ikwan

Ofishin mai gurfanar da kara a kasar Masar ya bayar da umarnin kama Shugaban kungiyar ’Yan uwa Musulmi ta Ikwan, Mohamed Badie, bisa tuhumar laifin…

Ofishin mai gurfanar da kara a kasar Masar ya bayar da umarnin kama Shugaban kungiyar ’Yan uwa Musulmi ta Ikwan, Mohamed Badie, bisa tuhumar laifin tayar da hankali a gaban hedkwatar zaratan sojin kasar, inda aka halaka mutum 55, kamar yadda Kamfanin dillancin Labarai na Gabas ta Tsakiya (MENA) ya ruwaito.
A cikin wannan umarni da aka bayar, an hada da manyan jami’an Ikwan, wadanda suka hada da mataimakin Badie, Mahmoud Ezzat da shugabannin jam’iyyarsu Essam El-Eriam da Mohammed El-Bletagi.
Dubban ’ya’yan kungiyar ’yan uwa Musulmi ta Ikwan, sun tare a wani Masallaci da ke Arewa maso Gabashin Alkahira, inda suke fafutikar ganin an sake mayar da Mohamed Mursi kan shugabanci, bayan da sojoji suka kifar da gwamnatinsa a makon da ya wuce.