✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An bindige tsohon kansila kan zargin leken asiri ga masu satar mutane

Sojoji sun bindige wani tsohon kansila kan zarginsa da yi wa masu garkuwa da mutane leken asiri a garin Dogon Dawa da ke Karamar Hukumar…

Sojoji sun bindige wani tsohon kansila kan zarginsa da yi wa masu garkuwa da mutane leken asiri a garin Dogon Dawa da ke Karamar Hukumar Birnin Gwari a Jihar Kaduna.

Tsohon kansilan ya nemi ya gudu ne lokacin da sojojin suka kama shi a garin Dogon Dawa inda suka harbe shi.

Wata majiya a garin ta shaida wa Aminiya cewa lamarin ya faru ne a ranar 16 ga  Yunin nan.

A cewar majiyar wacce ta nemi a sakaya sunanta ta lamarin ya bai wa mutanen garin mamaki.

“Kansilan sannanne a garin, kuma daya daga cikin mutanen da masu garkuwa da mutane suka sako ne ya ji yana waya da masu satar mutanen, inda aka ce yana fada masu cewa don me za su sako wani mutum da suka kama bayan mai kudi ne kuma har ’yan uwansa sun fara sayar da kadarorinsa domin su karbo shi?

“Bayan an sanar da sojoji ne sai suka  kama shi, kuma da ya ga sarari ne sai ya nemi ya gudu su kuma suka harbe shi,” inji majiyar.

Akwai kuma bayanai da ke danganta wanda ake zargin da hannu wajen ba da bayanan da suka yi sanadiyyar  sacewa tare da yin garguwa da wadansu Kiristoci 15  a yankin Dankande da ke  Dogon Dawa a makonnin baya.

Aminiya ta tuntubi Mukaddashin Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar Soji ta Daya da ke Kaduna, Kanar Ezindu Idimah, inda ya ce ba ya da labarin, amma zai bincika ya ji yadda abin yake kafin ya ce wani abu a kai, amma bai kira ba har aka hada wannan rahoto.