✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An bude Asibitin Ma’aikatan Shari’a na farko a Katsina 

A makon jiya ne Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya bude Asibitin Ma’aikatan Shari’a wanda ya zamo ta farko a  ma’aikatar a duk fadin…

A makon jiya ne Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya bude Asibitin Ma’aikatan Shari’a wanda ya zamo ta farko a  ma’aikatar a duk fadin Najeriya.

A jawabinsa, Babban Jojin Jihar Mai shari’a Musa Danladi Abubakar, ya ce ya yi tunanin gina wannan asibiti ne tun yana rike da mukamin magatakarda, amma Allah bai sa hakar ta cimma ruwa ba sai a lokacin wannan gwamnati. “Lokacin da na je wajen Mai girma Gwamna da wannan batu bai tsaya wata-wata ba wajen yarda da kuma bayar da damar gina wannan asibiti wadda kuma ga shi yau Allah cikin ikonSa Ya ba shi damar bude shi da kansa. Kamar yadda aka sani, rayuwa irin ta alkalai ta sha bamban da ta sauran al’umma saboda  nauyin da ke kansu, to babu dadi a ce alkali ya je asibiti su rika gogayya da wanda ya taba yanke wa hukunci a kan wani abin da shari’a ta ce a yi masa. Wanda aka yanke wa hukunci ba kallon shari’ar yake yi ba, alkalin yake kallo, to kuwa duk yadda alkalin ya so sai ya ji ba dadi domin haduwa ce a wani wuri na musamman ba kamar haduwar kasuwa ba, wadda kai ka kai kanka ba lalura ba kamar ta zuwa asibiti,” inji shi.

Ya ce, “Mun yi nazarin wanda ya kamata mu sanya sunansa a asibitin. Mun tabbatar da cewa babu wanda ya dace irin Mai shari’a Umar Abdullahi domin shi ne Babban Joji na farko a wannan jiha. Abu na biyu shi ne, duk lokacin da aka ga wani abu na jin dadin ma’aikata ya zo, to yana jinginar da nasa.”

Dangane da batun ma’aikata da likitoci da batun magani, Babban Jojin ya ce, tuni suka yi yarjejeniya da gwamnati kan wadannan abubuwa da sauran wasu shirye-shirye.

Shi kuwa Mai shari’a Umar Abdullahi wanda aka sanya wa asibitin sunansa, wato, Asibitin Ma’aikatan Shari’a na Mai Shari’a Umar Abdullahi (Justice Umar Abdullahi Judiciary Health Clinic) bayan nuna jin dadi da godiya, ya ce irin wannan aiki ba yinsa ke da wuya ba, sai dai yaya za a rike shi ta yadda zai ci gaba da aiki.

Mai shari’a Umar Abdullahi ya ja hankalin wadanda aka gina asibitin dominsu su tabbatar suna amfani da shi yadda ya dace.

Babban bako a wajen bude asibitin Babban Jojin Najeriya, Mai shari’a Muhammad Tanko Ibrahim, wanda ya samu wakilcin Mai shari’a Uwani Abba Aji ya ce ginawa da zuba kayan aiki a asibitin domin kula da lafiyar alkalai da sauran ma’aikatan shari’a da ya zamo na farko a kasar nan abin jinjinawa ne matuka don ganin alkalan sun tafiyar da ayyukansu cikin natsuwa.

Babban Jojin ya ce, “Ina kira ga sauran gwamnatocin jihohi su yi koyi da Gwamna Masari a kan irin wannan aiki.”

A jawabin Gwamna Masari ya ce, “Kula da batun kiwon lafiya da sauran hanyoyin jin dadi ga alkalai da sauran ma’aikatan sashin zai bayar da damar su yi aikinsu yadda ya dace.”

Gwamnan ya ce, asibitin zai bayar da kula a matakin farko na kiwon lafiyar alkalan da iyalansu da sauran ma’aikatan sashen. Ya ce, gwamnatinsa na mutunta sashen shari’a ta hanyar, “Biyan kudin hutu da magunguna da na tufafi da sauransu. Gwamnatin Jihar ta ba Babban Jojin Jihar amincewarta kan biyansu cikin lokaci, sannan an yi wa alkalan majistare da kotunan shari’a karin alawus, sannan nan bada jimawa ba za a samar musu da motocin hawa.” inji Gwamnan.

Asibiti yana da dakunan kwanciya biyu masu dauke da gadaje 6, wato bangaren maza da na mata.