✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An bude makarantu da tafiye-tafiye tsakanin jihohi

Gwamnatin Tarayya ta ba da izinin yin tafiye-tafiye tsakanin dukkan jihohin Najeriya. Gwamnatin ta kuma sanar da amincewar a bude makarantu ga dalibai da ke…

Gwamnatin Tarayya ta ba da izinin yin tafiye-tafiye tsakanin dukkan jihohin Najeriya.

Gwamnatin ta kuma sanar da amincewar a bude makarantu ga dalibai da ke shirin jarrabawar kammala karatun  firamare da sakandare.

Hakan na zuwa ne a ranar Litinin da Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi rahoto na biyar daga kwamitinsa na kar-ta-kwana kan yaki da cutar coronavirus, kan halin da ake ciki game da cutar a kasar.

“Ina farin cikin shaida muku cewa Shugaban Kasa… ya amince, sai dai ‘yan sauye-sauyen da za a sanar a nan gaba”. inji Bos Mustapha, shugaban kwamitin.

Sai dai ya ce tafiye-tafiyen za su fara ne daga ranar 1 ga watan Yuli, tsakanin karfe 5 na Asuba zuwa 10 na dare da a baya aka kebance manyan motoci masu dakon kayan abinci da kayan gwari da shi.

Za a bude makarantu

Boss Mustapha ya kara da cewa Shugaba Buhari ya amince a bude makarantu ga daliban ‘yan aji shida na firamare, da kuma ‘yan aji uku na karamar sakandare da kuma ‘yan aji uku na babbar sakandare da ke shirin jarabawar kammala karatu.

Sai dai ya kara da cewa nan gaba za a sanar da matakan da za a bi wajen bude makarantun.

Ya kuma ce gwamantin ta amince da bude filayen jirgin sama cikin matakan kariyar cutar coronavirus.
Jawabin Boss Mustapha ya ce sassaucin na makonni hudu bai hada da sauran tarukan jama’a a.