✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An bukaci ‘yan kasuwa su zabi shugabanni nagari a zaben 2019

Shugaban ’yan Kasuwar ’Yan Lemu da ke Maraba a Karamar Hukumar Karu a Jihar Nasarawa, Alhaji Hussaini Abdullahi ya bukaci mambobin kasuwar su tabbatar sun…

Shugaban ’yan Kasuwar ’Yan Lemu da ke Maraba a Karamar Hukumar Karu a Jihar Nasarawa, Alhaji Hussaini Abdullahi ya bukaci mambobin kasuwar su tabbatar sun zabi ’yan siyasa nagari da ke da kishin ci gaban al’umma baki daya musamman su ’yan kasuwa. Shugaban ya yi wannan kira ne a lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu a ofishinsa da ke kasuwar a ranar Talatar da ta gabata, inda ya ce kiran ya zama wajibi musamman a yanzu da zabubbukan 2019 ke gabatowa. Ya ce ’yan siyasa da dama masu halaye daban-daban na nuna sha’awarsu ta tsayawa takarar kujeru daban-daban a jihohi da kasa baki daya. Saboda haka a cewarsa ya rage ga jama’a musamman ’yan kungiyar da ’yan kasuwar baki daya su tantance ’yan takarar su ga wanda ya dace su zaba a lokutan zabubbukan.

Abdullahi, ya ja hankalinsu  cewa lokaci ya wuce da za su bar wadansu ’yan siyasa masu son kansu su rude su da kudi da alkawuran karya don su zabe su bayan sun yi nasara kuma su manta da su sai kuma lokacin wani zaben.