Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

An bukacin gwamnatin Buhari ta gyara hanyar Jos zuwa Kaduna

Alhaji Hamisu Rabi’u Mai Manja Saminaka
Alhaji Hamisu Rabi’u Mai Manja Saminaka

Wani dan kasuwa da ke garin Saminaka a Jihar Kaduna, Alhaji Hamisu Rabi’u  Mai Manja Saminaka ya yi kira ga Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, kan ta gyara hanyar da ta taso daga Jos zuwa Kaduna domin ceto al’ummomin da suke bin wannan hanya, daga mawuyacin halin da suke ciki sakamakon lalacewar  hanyar.

Alhaji Hamisu Rabi’u Mai Manja ya yi wannan kira ne a lokacin da yake zanta wa da wakilin Aminiya a Jos.

ADVERTISEMENT

Ya ce gaskiya mutane suna matukar shan wahala a wannan hanya sakamakon lalacewar da ta yi shekara da shekaru, musamman lokacin damina.

Alhaji Hamisu Mai Manja ya yi bayanin cewa wuraren da wannan hanya ta fi mugun lalacewa, sun hada daga garin Saminaka zuwa Jos da daga garin Pambeguwa zuwa Saminaka da kuma daga Gadar Gayan zuwa garin Panbeguwa.

ADVERTISEMENT

Ya ce wannan hanya ta kai sama da shekara  20 da lalacewa, domin tun lokacin Gwamnatin Obasanjo aka ce an bayar da aikin wannan hanya suka ji shuru.

Ya ce Gwamnatin Goodluck ta zo ita ma aka ce an bayar da aikin wannan hanya, nan ma suka ji shuru.

‘’Wannan hanya tana bada gagarumar gudunmawa wajen tattalin arzikin kasar nan. Domin ta hada jihohin Borno, Gombe, Adamawa, Bauchi da Filato. Kuma  mutanen da suke bin wannan hanya, suna dauko kayayyakin amfanin gona kamar  wake da masara da shanu da taki, da sauran kayayyakin harkokin kasuwanci.”

Ya ce suna murna cewa wannan gwamnati ta su ce, domin sun zave Shugaban Kasa Buhari dari bisa dari amma sun yi shekara 4 ba a gyara wannan hanya ba.

Don haka yake rokon Gwamnatin Buhari da dukkan sauran masu hannu kan wannan al’amari, su kawo dauki kan gyaran wannan hanya, domin a ceto jama’ar da suke bin wannan hanya, daga mawuyacin halin da suke ciki.