Da Dumi Dumi

An bullo da sabon tsari a gasar Firimiyar Ingila

Daga kakar wasa ta bana Hukumar Kwallon Kafa a Ingila (FA) za ta fara amfani da sabon tsari a gasar Firimiya ta Ingila.

Za a fara gasar ta bana ce a ranar 9 ga watan Agusta mai zuwa.

Hukumar ta ce daga bana, za a rika amfani ne da tsarin wa ya fi karfin wai a gidansa (Head-to-Head) ga duk kungiyoyin da suka yi kankankan da juna a gasar maimakon tsarin da ake bi na duba kungiyar da ta fi yawan zura kwallaye a raga.  Ma’anar Head-To-Head shi ne za a yi amfani da sakamakon wasannin gida-da-waje ga kungiyoyin da suka yi kankankan da juna.

Hukumar ta ce wannan tsari zai shafi kungiyoyin da suka yi canjaras ne a kokarin lashe gasar ko neman matsayi na hudu ko neman hayewa Gasar Cin Kofin Europa wato na 5 da na 6 da kuma matakin koma baya wato na 17 da 18 da na 19.

Wannan ne karo na farko da za a fara amfani da wannan tsari a gasar Firimiya ta Ingila.  Amma tuni ake amfani da shi a gasar La-Liga ta Sifen da wasu gasanni a Nahiyar Turai.

ADVERTISEMENT

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Share