✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An cafke barayin shanu biyu a Edo

A farkon makon nan ne wasu barayin shanu biyu da suka addabi ’yan kasuwa a Jihar Edo suka shiga komar jami’an tsaro, bisa taimakon ’yan…

A farkon makon nan ne wasu barayin shanu biyu da suka addabi ’yan kasuwa a Jihar Edo suka shiga komar jami’an tsaro, bisa taimakon ’yan bangar jihar.
barayin, Muhammad Muhammad dan shekara 40 da Musa Bulama dan shekara 30, asirinsu ya tonu ne a lokacin da suka hada baki suka ware wani tikeken bajimi a cikin shanun kiwon Muhammad Jibir, suka sace shi, suka kai wa wata mahauciya, wadda ba a ambata sunanta ba a hanyar zuwa Sapele.
Bincike ya tabbatar da cewa, tun da farko sai da shi Muhammad Muhammad din ya je garken Alhaji Muhammad Jibir a wani lokaci can baya cikin dare, inda ya gana da abokinsa Musa Bulama gainakon shanun, daga nan sai ya tafi ba a sake jin duriyarsa ba sai a wannan karon. Ya sake zuwa ya hadu da wannan abokin nasa, inda suka hada baki, suka aikata satar.
Wanda ake zargin, Muhammad Muhammad ya ce shi dan kabilar Shuwa-Arab ne daga Jihar Borno, yana da zama a garin Dakwa ne da ke Abuja. Ya ce yana da matar aure da ’ya’ya biyu. “Aikina kiwo, ba ni da wani aiki bayan wannan, domin fadan ’yan kungiyar Boko Haram ne ya tilasta muka bar yankinmu, muka dawo Abuja. Wannan tsautsayin da ya fada mani, ku yi mani afuwa. Ni ban taba yin sata ba.” Inji shi.
Wadanda ake zargin dai suna tsare a ofishin ’yan banga, kamar yadda shugabansu, Alhaji Shu’aibu Muhammad KT ya shaida wa wakilinmu. “Muna tsare da wadanda ake zargin dukkansu biyu, amma za mu mika su ga hukumar ’yan sanda. Bukatarmu ga masu shanu da sauran jama’a, su ba kungiyarmu ta ’yan banga hadin kai, ta hanyar bayanan sirri na gaskiya game da masu aikata miyagun ayyuka; domin zakulo su duk inda suka boye.” Inji shi.