✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An cafke masu kai wa Boko Haram makamai

Rundunar tsaro ta NSCDC ta kasa reshen Jihar Borno ta kama mutum hudu da zargi yi wa kungiyar Boko Haram jigilar aiki da jarkoki 34…

Rundunar tsaro ta NSCDC ta kasa reshen Jihar Borno ta kama mutum hudu da zargi yi wa kungiyar Boko Haram jigilar aiki da jarkoki 34 makare da man fetur.

Kwamandan NSCDC a jihar, Ibrahim Abdullahi ya bayyana hakan a lokacin da yake bajekolin wadanda ake zargin.

Ibrahim ya ce daya daga cikin wadanda ake zargin mai gidan mai ne a kauyen Husara da ke Karamar Hukumar Askira/Uba ta Jihar Borno.

Sauran wadanda ake zargin su uku wadanda aka kama ne a Karamar Hukumar Michika ta Jihar Adamawa.

Ya ce kayan da aka kama din sun hada da jarkokin man fetur 34 dauke da lita 880 na mai a kan babura.

Kwamandan ya ce shiyyar ta magance matsaloli kusan 1,318 a bana, inda daga ciki aka warware 734 yayin da 468 kuma har yanzu ake ci gaba da bibiyar su.