✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ci gaba da tsare wani mawaki a Kano

A ranar Larabar da ta gabata ne kotun tafi-da-gidanka a karkashin Hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano ta sanya aka ci gaba da tsare wani…

A ranar Larabar da ta gabata ne kotun tafi-da-gidanka a karkashin Hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano ta sanya aka ci gaba da tsare wani mawaki mai suna Rabi’u wanda aka fi sani da “Taka Lafiya” bisa zarginsa da laifin fitar da wata waka mai taken “Barhama Nake Bautawa” ba tare da hukumar ta tace ba.
Tun farkon zaman kotun wanda aka yi a ranar Juma’ar da ta gabata Mai shigar da karar babban lauyan gwamnati Hussaini Hassan ya ce mawakin ya rera wakar tare da fitar da ita don sayarwa a kasuwa ba tare da an tace ta a hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano ba, inda ya ce hakan laifi ne da ya saba wa sashe na 100 (2) da na 90 (1)(a) na kundin dokokin harkar sinima ta Jihar Kano na shekarar 2001, wanda kuma laifi ne da za a hukunta wanda ya aikata shi a karkashin sashe na 112 na wannan dokar.
Haka kuma ya ce ana zargin mawakin a cikin wakarsa da cewa yana bauta wa shugaban darikar Tijjaniya Shaikh Ibrahim Inyass.
Mai shigar da karar ya bayyana cewa lokacin da mawakin ya samu takardar gayyata, sai ya gudu Jihar Nassarawa inda aka kama shi a can sannan aka damka shi a hannun ‘yan sanda na Abuja.
A lokacin da aka karanta wa wanda ake zargin laifuffukansa a gaban kotu, ya ki yarda da laifinsa. A nan ne kotun ta dage saurarar shari’ar zuwa ranar Litinin 3 ga watan Yuni tare da bayar da umarnin ci gaba da tsare wanda ake zargin har zuwa wannan lokaci.
Lokacin da aka sake zaman kotun a ranar Litinin din mawakin ya amsa laifinsa tare da neman kotu ta tausaya masa wajen yanke masa hukunci.
A nan ne Alkali Muktar Ahmed ya sake dage shari’ar zuwa 5 ga watan Yuni da nufin yanke wa wanda ake zargin hukunci.
Da aka sake zaman kotun a ranar Laraba ne sai mawaki Rabi’u “Taka lafiya” ya canza maganarsa, inda ya musanta zargin da ake yi masa. Haka kuma lauyansa mai suna Mohammed Mustapha Hussaini ya shaida wa kotun cewa ba ta da hurumin saurara karar, kasancewar wai ya aikata laifin ne a Lafiya ta Jihar Nasarawa. A cewarsa kuma wata babbar kotu a Abuja ta bayar da umarnin kada wata kotu ta sake saurarar karar.
A nan ne lauyan wanda ake zargin ya nemi kotu ta dage wannan shari’a  zuwa 18 ga wata Yuni.
Bayan saurarar dukkanin bangarorin biyu, Alkali Muktar Ahmad ya dage zaman shari’ar zuwa 18 ga watan Yuni kamar dai yadda alkalin wanda ake zargi ya nema tare da bayar da umarnin ci gaba da tsare wanda ake zargi a gidan wakafi.
A wannan zaman, kotun ta cika makil da jama’a wadanda ke son jin hukuncin da alkalin zai yanke, kasancewar shari’ar ta ja hankalin jama’a, sakamakon irin cece-kucen da ta haifar a wurin jama’ar jihar wadanda mafi yawansu Musulmi ne.